Al’ummar yankin Kerawa dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, sun bayyana cewa ya zuwa yanzu garuruwa sama 30 aka gudu aka bari saboda hare-haren ‘yan bindiga.
Da yake magana da Sashen Hausa, Kansilan dake kula da yankin, Alhaji Dayyabu Kerawa, ya ce yanzu haka akwai sama da mutane 100 a hannun masu garkuwa da mutane.
Matsalar tsaron dai na karuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan bindiga su ka yi alkawarin ajiye makamansu, lokacin da Shiekh Ahmed Gumi, ya zauna da su. Sai dai Mazauna yankin na cewa lamarin ma kara dagulewa ya yi.
Ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Ahmed El-Rufa’i, ya karbi wani rukunin sojoji mata da aka kai jihar domin taimakawa da ci gaba da ayyukan samar da tsaro.
Yankunan Birnin Gwari da Giwa da kuma Igabi na fama da matsalolin tsaro a jihar Kaduna. Yanzu haka dai shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sauya shugabannin tsaron kasar, wanda ake fatan hakan zai samar da zaman lafiya.
Saurari cikakken rahotan Isah Lawal Ikara.