Wata tawagar masana ilimin kimiyya a Hukumar Lafiya ta Duniya wadda ke binciko asalin kwayar cutar Korona, wadda ta fara bayyana a lardin Hubei na kasar China, a karshen shekarar 2019, ta ziyarci wata cibiyar kula da cututtuka a lardin jiya Litinin, inda ta kasance muhimmiyar cibiya wajen kula da yaduwar cutar a farkon bullarta.
China, ba ta fitar da wani cikakken bayani ba game da ziyarar tawagar, zuwa Cibiyar Kula da Cututtuka ta lardin Hubei. Mamba a kungiyar, Peter Daszak, ya fada wa manema labarai cewa “taron ya kasance mai matukar muhimmanci.”
Tun da isar wannan tawagar ta WHO a watan jiya, masana kimiyyan sun kuma ziyarci Kasuwar Namun Ruwa Ta Huanan, wacce ke da nasaba da tarin kwayoyin cutar COVID-19, da kuma a kalla daya daga cikin asibitocin da ke Wuhan, wadanda suka kula da wasu daga cikin marasa lafiya na farko. COVID-19 ita ce cutar da Korona bairos ke haifarwa.
Masana kimiyyar suna so su san inda kwayar cutar ta samo asali, kuma a jikin wace dabba da yadda ta shiga cikin mutane - wani abu da zai iya daukar shekaru kafin a gano shi.