Jami'ai a Afurka sun ce suna aiki don samo daruruwan miliyoyin alluran rigakafi ga nahiyar a cikin shekara mai zuwa, kuma suna kira a hada kai a Afurka a yakin da ake yi cutar coronavirus.
Nahiyar Afurka na da mutane miliyan 3.4 da aka tabbatar sun kamu da cutar tun farkon bullowarta a watan Fabrairun bara. Tun daga wannan lokacin, Dr. John Nkengasong ya ce cibiyoyin kiwon lafiya a duk fadin nahiyar sun gudanar da gwaje-gwaje har miliyan 30 - mafi yawansu a cikin kasashe 10, ciki har da Afurka ta Kudu, kasar da ta fi sauran kasashen Afurka fama da cutar ta coronavirus.
Kasashen Habasha, Najeriya, Kenya, Zambiya da Uganda, suma duk sun gudanar da gwajin.
Dakunan gwaje-gwaje ‘kasa da 500 ne kawai a fadin nahiyar ke gudanar da gwajin cutar. Nkengasong ya ambaci kasashe hudu da suka fara rigakafin cutar a kwanan nan, da suka hada da Maroko (Morocco) da Masar da Seychelles da kuma Guinea.