Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sallami Shugaban Hukumar Dake Kula Da Muryar Amurka


Tsohon shugaban hukumar USAGM, Michael Pack.
Tsohon shugaban hukumar USAGM, Michael Pack.

Shugaban Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Amurka, USAGM ya sauka da yammacin jiya Laraba bisa bukatar gwamnatin Shugaba Joe Biden, jim kadan bayan da Biden ya hau mulki.

Michael Pack, ya yi aiki na tsawon sama da watanni bakwai na masu cike da wahalhalu a matsayin shugaban zartarwa na farko na hukumar a karkashin sabuwar doka da ta ba shi damar fadada ikonsa a kan kafafen yada labarai.

Tsohon mai shirya fina-finai mai ra'ayin mazan jiya ya yi fama da kararraki da koke-koke da kuma sammaci daga Majalisar Amurka, har ma da umarnin kotu da ke hana shi yin katsalandan kan ayyukan cibiyoyin sadarwa da yake kula da su, ciki har da Muryar Amurka da Asusun Fasaha OTP, wanda ke tallafa wa 'yancin yanar gizo a duniya.

A wata sanarwa ta ban kwana ga ma'aikatansa, Pack ya ce ya "mai da hankali ne kawai kan sake fasalin hukumar zuwa ga ayyukan da take yi” kuma don taimaka wa hukumar ta watsa labarin Amurka ga duniya da idon basira ba tare da son zuciya ba." Pack ya kara da cewa ya yi imanin "an samu kwaskwarimar da ya kamata" a karkashin jagorancinsa.

Yanwancin matakan da ya dauka, masu suka sun yi Allah wadai da shi a Majilisar Dokoki da masu kare 'yan cin ‘yan jarida da kungiyar masu tono asiri.

A wata wasika da magoya bayan Pack suka raba, dake nuna takardar murabus din sa ce, Pack ya bayyana bukatar gwamnatin Biden ta murabus din, a matsayin "bita da kullin siyasa." Pack ya kara da cewa tabbatarwar da Majalisar Dattijai ta yi masa ta kasance na wa'adin shekaru uku ne, domin tabbatar da cewa shugaban hukumar "ba a taba shi" ta dalilin sauye-sauye a harkokin mulki ba.

Canjin gwamnati, galibi na nufin sauya yawancin jama'ai, wadanda aka nada a siyasance da kuma wasu manyan jami'ai. Murabus din na Pack ya zo ne yayin da sauran jami'ai da yawa na tsohon Shugaban kasa Donald Trump suka yi murabus yayin da sabuwar gwamnatin ta fara aiki.

XS
SM
MD
LG