Jiya Lahadi an fara jigilar sabbin alluran rigakafin coronavirus ta jiragen sama daga kamfanin hada magunguna na Pfizer dake garin Kalamazoo, na jihar Michigan, zuwa sassa da yankunan kasar Amurka.
Shahararren mai kwarmaton nan na Najeriya, Dr. George Uboh, ya sami gayyatar Majalisar Wakilan Najeriya don ba da bahasi kan zargin salwantar kudi sama da dala Biliyan 35 a ma'ajiyar gwamnatin tarayya.
Amurka, ta sa sunan Nijeriya cikin jerin sunayen kasashen da su ka gaza ta bangaren yancin addini, wanda hakan ya share fagen yiwuwar sakawa Najeriyar takunkumi, muddun ba ta kyautata al’amuranta ba.
Mayakan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ke fama da tashe-tashen hankula, sun yi awon gaba da wani ma'aikacin agajin jin kai da wasu jami'an yanki biyu, a cewar jami’an tsaro a ranar Laraba.
Zababben shugaban Amurka, Joe Biden da Mataimakiyar Shugaban mai jiran gado Kamala Harris, sun sanar da nadin tawagar mata zalla a fannin sadarwa.
Ziyarar wasu gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, na ci gaba da tada kura a fagen siyasar kasar.
Fitaccen dan siyasar Sudan, kuma tsohon Fira Minista Sadiq al-Mahdi, ya mutu ne sakamakon fama da cutar Coronavirus makonni uku bayan da aka kwantar da shi a Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar wata sanarwa da jam'iyyarsa da kuma iyalansa suka fitar da safiyar yau Alhamis.
Tabarbarewar tsaro a Najeriya ya sa Majalisar Dattawa ta umarci kwamitin Sadarwa ya gaiyaci ministan Sadarwa, Dakta Ali Isa Pantami, domin a fahimtar da shi bukatar samar da mafita.
A Najeriya al'ummomin da ke fama da rashin tsaro sun fara kulla kawance domin kare jihohinsu daga barazanar ‘yan ta'adda.
Hukumar da ke hidima ga cibiyoyin gwamnatin tarayyar Amurka (GSA a takaice), ta tabbatar cewa zababben shugaban kasa Joe Biden, shi ne a ta bakinta, “wanda, ga alama ya yi nasara” a zaben ranar 3 ga watan Nuwamba.
'Yan bindigar da suka sace daliban Sashen Harshen Faransanci na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Lahadi, na neman kudin fansa Naira miliyan 450 daga wajen ‘yan uwan daliban.
Birnin New York ya umarci makarantu su rufe ranar Laraba, yayin da garin ya sami karin yawan masu kamuwa da coronavirus kwanaki bakwai a jere sama da kashi uku cikin 100.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce hukumar na, a ta bakinsa, “matukar damuwa” da yadda cutar coronavirus ke ta yaduwa, musamman ma a Turai da Amurka.
Jiya Lahadi, a karon farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna ya amince da cewa dan takarar Demokrat Joe Biden "ya lashe" zaben shugaban kasa kusan makonni biyu da suka gabata, amma sanadiyyar magudi.
Gwamnatin jihar Sokoto tare da hadin gwiwar kungiyar tsofaffin daliban cibiyar nazarin dubarun shugabanci dake garin Kuru Jos sun tattaunawa don samar da mafita ga matsalar tsaro.
Babban jami’in zabe a jihar Georgia da ke kudancin Amurka ya ba da umarnin a sake kidayar kuri’un zabe da hannu wanda aka yi tsakanin Shugaba Donald Trump da zababben Shugaban Joe Biden.
Tun rasuwar marigayi mai yaki da miyagun barayi, Alhaji Ali Kwara a ke ci gaba da nuna juyayin rashin sa, inda kafafen sadarwar yanar gizo su ka cika makil da ta'aziyar rasuwar mutumin da a ke aiyanawa a matsayin mai Jarumi.
Akalla mutane uku sun ji rauni ranar Laraba lokacin da wani bam ya tashi a wurin bikin tunawa da ranar tsoffin sojoji da ‘yan kasashen waje suka halarta a makabartar da ba ta musulmi ba a garin Jiddah na Saudiyya, a cewar wata sanarwar da hukumomi suka fitar.
Gwajin rigakafin cutar coronavirus da kamfanin Pfizer ya samar, ya nuna sakamako mai kyau da ya wuce yadda aka yi tunanin samu a baya.
Har yanzu gwamnatin Amurka ba ta fara batun mika mulki ga wanda aka yi hasashen zai lashe zaben shugaban kasar Amurka ba.
Domin Kari