Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Amurka Ta Sake Tsige Shugaba Donald Trump


Shugabar Majalisar Wakilai Nancy Pelosi.
Shugabar Majalisar Wakilai Nancy Pelosi.

A karo na biyu cikin wa'adin mulkinsa na shekaru hudu Majalisar Wakilan Amurka ta sake tsige shugaban kasa Donald Trump. Kuma zai fuskanci shari'a a Majalisar Dattawa bayan sabon shugaban kasa ya fara aiki.

Ranar Laraba ‘yan Majalisar Dokokin Amurka sun sake tsige shugaban kasa Donald Trump, akan dalilin haddasa rikici a makon jiya, inda ya umurci magoya bayan sa da su yi tattaki zuwa ginin Majalisa don dakatar da tabbatar da sakamakon zabe, inda mafusatan magoya bayansa suka yi bore suka hargitsa Majalisar da ya kai ga mace-mace.

Kuri’un masu rinjaye 232 ne suka amince da a tsige shi, kana kuri’u 197 suka ki amincewa da hakan, a dai-dai lokacin da ya rage mishi mako guda ya sauka daga kujerarsa na wa’adin shekaru 4, ‘yan jam’iyyar Trump ta Republican mutum 10 ne suka sa hannu a kan a tsige shi.

Kuri’ar dai ta sa Trump a matsayin shugaban kasa na farko cikin shugabannin kasar su 45, da aka taba tsigewa har sau biyu, a cikin tarihin kasar shekaru 245.

A shekarar da ta gabata ne dai Majalisar dattawan kasar ta wanke shi akan wasu zarge-zargen, yanzu kuma zai fuskanci wata tuhumar bayan sabuwar gwamnatin Joe Biden ta kama aiki, a ranar Laraba mai zuwa. Abin da kawai da za a bukata a Majalisar Dattawan shine, kashi biyu cikin uku su sa hannu sai a tabbatar da tsigewar.

Idan kuma aka tabbatar da tsigewar, hakan zai sa ba zai sake rike wani ofishin gwamnati ba har abada.

Tsigewar ta zo mako kuda bayan zanga-zangar da aka yi a Majalisar kasar, inda masu zanga-zangar suka sha karfin ‘yan sanda a cibiyar Dimokaradiyar Duniya, a lokacin da ‘yan Majalisun ke tabbatar da zaben wakilan Electoral College, wanda ke nuna cewar Joe Biden ya kada Trump a zaben watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG