Gamayyar kungiyoyin Arewa dai ta kira taro ne don bayyana matsayinta game da maganar matsalar tsaro, musamman kan abin dake faruwa a Kudancin Najeriya, inda ake barazanar korar wasu Fulani.
Daraktan kungiyar ta CNG, Kwamarad Aminu Adam, ya bayyana cewa suna shirin fara taron a wani wurin shatawa na NAF Club da ke Kadunan, sai ma’aikatan wajen suka ce an basu umarnin dakatar da su, kuma kan hanyarsu ta ficewa ne wasu jami’an tsaro suka kama shugabannin kungiyar biyu.
Shugabannin biyu da aka kama su ne Nastura Shariff da Balarabe Rufai, wadanda yanzu haka babu wanda ya san inda suke, kuma wayoyinsu a kashe.
Maganar matsalar tsaro da kuma barazanar korar Fulani daga wasu jihohin Kudu, ta sa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa'i jan hankalin al’umma da su bar jami’an tsaro su yi aikinsu.
El-Rufa’i ya ce babu tabbacin ingancin hotunan bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta.
A baya dai kungiyar ta CNG ta taba barazanar korar ‘yan kudancin kasar dake zaune a Arewa, saboda yadda ‘yan Kudu su ka bada wa’adin korar ‘yan Arewa daga yankinsu.
A wancan lokacin gwamnatin jihar Kaduna ta saka kafar wando daya da wannan kungiya. Lamarin da ya sa ‘yan gamayyar kungiyar ke ganin gwamnatin ce ta watsa musu taro.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.