Daidai lokacin da guguwar siyasa ke kara kadawa a Najeriya, ‘Yan kasar na ganin cewa kasar tana bukatar haziki kuma gogagge a dukkan fannonin ayyukan gwamnati wanda shi kadai kan iya kai ta ga tudun mun tsira.
Wannan na zuwa ne lokacin da masu neman tsayawa takarar shugabancin kasar ke ta nuna anniyar su ga jama'a.
Kasancewar wannan shekara ta 2022 shekarar da ke bi ma shekarar da za'a gudanar da zabbuka a Najeriya ya sa guguwar siyasa ke ta kadawa a matakai daban-daban a jam’iyyu daban- daban.
Wani abu da ke jan hankalin ‘yan Najeriya bai wuce batun shugabancin kasar ba, inda wasu ke ganin ya kamata a yi karba-karba tsakanin yankin kudu da yankin arewa, wasu kuma na ganin akasin hakan.
Wannan dai bai hana masu niyar neman shugabancin kasar ba nuna anniyarsu a bainar jama'a ba, na bayan bayan nan ga nuna ra'ayi shi ne gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.
Daga cikin masu neman shugabancin Najeriya, kowane yana ganin ya cancanta neman mukamin bisa nasa dalilai duk da yake ba lallai ne wasu su gamsu da dalilan ba.
Shugabancin kasa a cewar wasu ‘yan kasar na bukatar shugaba wanda watakila aka gwada kuma aka gamsu da iyawar sa, akan hakan ne ma wasu ‘Yan Jiha suka tofa albarkacin bakin su akan ra'ayin da gwamna Tambuwal ya nuna.
Alhaji Umarun Kwabo A. A, gogaggen dan siyasa ne a Sokoto.
“Duk wanda ya kasance dan Jihar Sokoto, ko wani lungu da sako ka tambaye shi zai ba ka shaidar ayyukan akhairi da wannan gwamnatin ta yi. Har wani mawaki na ji yana waka yana cewa jan wasu jihohi cewa su wane sai an zo sokoto a hau flyover.
Yanzu dai ana iya cewa kakar siyasa ce ta kama ka’in da na’in a Najeriya, domin tuni ‘Yan kasar fara lissafin lokacin babban zabe da za’a yi a shekara mai zuwa ta 2023.
A kwanakin baya tsohon gwaman jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar a zaben 2023.
A lokacin da ya bayyana aniyarsa, Tinubu ya ce shi ne mutumin da ya dace ya gaji shugaba Buhari saboda irin rawar da ya taka a lokacin yana shugabancin Legas.
Sannan akwai tsohon gwaman jihar Imo Rochas Okorocha da shi ma ya bayyana ra’ayinsa a baya-bayan.