Yanayin rashin tsaro a kasar yana daukar wani salo wanda masu fashin baki ke kallo da fuskoki dabam daban.
Tun lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka fara fatattakar ‘yan bindiga a wasu wurare kamar yankin gabashin jihar Sokoto musamman garin Isa, inda aka kona motar wasu matafiya har suka mutu, mazauna yankunan sun ce ana samun saukin hare-haren ‘yan bindiga, kamar yadda masanin al’amuran yau da kullum Bashir Altine Guyawa ya bayyana.
Shi ma wani mazaunin yankin da ya so a sakaya sunansa, ya ce akwai saukin hare-haren amma kuma akwai wani ‘dan bindiga da har yanzu ya ke addabar wasu yankunan garin na Isa.
A garin Illela dake gabashin Sokoto, mazauna yankin sun ce akwai alamun ‘yan bindigar da ake fatattaka a yankin Isa sun soma kwararawa wani daji dake tsakanin garin Illela da Gwadabawa.
Detective Auwal Bala Durumin Iya, shugaban sashen nazarin aikata laifuka da tsaro a jami'ar Yusuf Maitama Sule dake Kano, ya ce sakin wasu mutane da shahararren dan bindiga Bello Turji ya yi, wata dabara ce ta neman afuwa daga gwamnatin tarayya domin ya ga an takura mashi.
Dama dai masana sun jima suna bayar da shawarwari akan cewa idan za'a murkushe ‘yan bindiga to a tunkaresu gaba daya, domin gudun kada wasunsu su yi kaura zuwa wani wuri su ci gaba da aikata ta'asa.
Saurari rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti: