Wani rikice ne ya kunno kai inda har babbar Jam'iyar adawa ta PDP ke shirin daukar mataki da doka akan yunkurin hana ta shiga zaben kananan hukumomi da za'a gudanar a jihar kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya gobe asabar 5 ga watan Fabrairu 2022.
Hukumar Zabe ta jihar ce ta aikewa jam'iyar da takararda mai dauke da sa hannun sakatarenta Yahaya A. Riskuwa mai nuni akan cewa, jam'iyar ta saba wasu dokoki ta cancantar shiga zabe ana kasa da sa'a 48 kafin soma zabubukan.
Dokokin da jam’iyar ta saba a cewar hukumar sun hada da rashin biyan kudin fom na ‘yan takara cikin lokaci, sauya-sunayen wasu ‘yan takara a makare da kuma takardun da wasu ‘yan takara suka rubutawa hukumar na janyewa daga takara kai tsaye.
Yanzu dai jama'a sun zura ido domin ganin yadda zata kaya ganin ko bayan rikicin PDP da PRP ita kanta APC dake mulkin jihar tana fuskantar rikicin cikin gida tsakanin bangaren tsohon gwamna sanata Adamu Aliero da bangaren gwamna mai ci Sanata Abubakar Atiku Bagudu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: