Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hauhawar Farashin Dalar Amurka A Najeriya Na Ci Gaba Da Kawo Cikas Ga ‘Yan Kasuwa


Kayan Marmari Abinci
Kayan Marmari Abinci

Hauhawar farashin dalar Amurka na ci gaba da kawo babban cikas ga ‘yan kasuwar a Najeriya musamman wadanda ke fitar da kaya zuwa kasashen duniya.

A wani yunkuri na nemo bakin zaren samun sauki ga matsalar, ‘yan kasuwa na kasashen Afirka ta Yamma da ta tsakiya sun hadu domin neman mafita.

A tsarin hada-hadar kasuwancin da ke bukatar tura kudade daga wata kasa zuwa wata tsakanin kasashen duniya ana amfani ne da dalar Amurka wajen tura kudaden. Sai dai kuma wannan tsarin yakan kawo koma-baya ga wasu ‘yan kasuwa da ma kayan da suke fitarwa kasashen duniya musamman a kasashen da darajar kudin su ke zubewa kamar Najeriya.

Misali a haujin noma wanda gwamnatin kasar ke ikirin son bunkasawa, Najeriya ita ce ta biyu wajen samar da albasa mafi yawa ga kasashen Afirka ta yamma da ta tsakiya, kuma gwamnatin kasar ta amincewa masu kasuwancin ta, su fitar da ita ta wasu iyakokin kasar zuwa kasashen waje, sai dai a cewar shugaban manoma da kasuwancin ta a Najeriya Aliyu Maitasamu Isa, suna fuskantar babban kalubale.

Wani kalubale shine sufurin albasa salum-alum tsakanin kasashe, kuma ga karamcin kamfunan da zasu sarrafa ta ko kuma hanyar adana ta kar ta lalace, abinda yasa masu jagorancin hada-hadar ta a Afirka ke jaddada kira ga gwamnatocin kasashen su.

Duk da wadannan kaluballen wasu na ganin idan aka hada kai wuri daya za'a iya samo bakin zaren saukakawa masu tu'ammuli da wannan amfanin gona.

A wannan lokacin da gwamnatin Najeriya ke tinkaho da habaka noman abinci cikin kasar, samar da mafita ga kalubalen da ke tarnaki ga hada-hadar kasuwancin kayayyakin amfanin gona zai iya taimakawa kudurin gwamnatin ko akasin haka.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Hauhawar Farashin Dalar Amurka A Najeriya Na Ci Gaba Da Kawo Cikas Ga ‘Yan Kasuwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG