Hadin kan ‘ya'yan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na ci gaba da zama wani babban tarnaki da ya dabaibaye jam'iyar a sassa daban-daban na kasar.
Daidai lokacin da kwamitin sulhu da jam'iyar ta kafa a matakin kasa ke kai-komo wajen sasanta rikice-rikicen da suka biyo bayan zabubukan da suka gabata, matsalolin sai kara dagulewa suke yi a wasu jihohin kasar.
A jihar Kebbi wadda ke arewa maso yammacin kasar, an dauki tsawon watanni ana samun takun-saka tsakanin ‘ya'yan jam'iyyar duk da yake an jima ana taushe batun.
Yanzu dai a iya cewa abin da ke boye ya fito fili domin masu goyon bayan bangaren Tsohon gwamna Sanata Muhammad Adamu Aliero sun yi gangamin tarbon jigon nasu, lokacin da su ko magoya bayan Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu suka himmantu wajen shirye-shiryen zabukan kananan hukumomi da za'a gudanar a jihar.
Sanata Adamu Aliero ya maganta da dandazon jama'ar da suka tarbo sa tun daga filin jirgi har zuwa sabon ofishin da suka buda a garin Birnin kebbi bayan dawowar shi daga wurin duba lafiyarsa.
A bangaren masu goyon bayan gwamna sanata Abubakar Bagudu kuwa jam'iyyar APC a jihar Kebbi daya ce, kuma ba su hana a tarbo Adamu Aliero ba a cewar sani Zauro Dattijo a cikin jam'iyyar.
Rikice-rikicen cikin gida a jam'iyun siyasa ba sabon abu ba ne a cewar masanar kimiyar siyasa musamman a kasashe kamar Najeriya irinsu Farfesa Abubakar Abdullahi na sashen nazarin kimiyar siyasa a jami'ar Usmanu Danfodiyo .
Masana na ganin cewa samun nasarar hada kawunann ‘ya'yan jam'iya wuri daya yana da tasiri wajen samun nasarar jam’yar da ma samar da shugabanci managarci ko kuma akasin haka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: