Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Dora Haraji Bayan Sun Kai Hari Garuruwan Arewacin Najeriya


‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Jama'a na ci gaba da shiga kunci sanadiyar ayyukan ‘yan bindiga da ke ci gaba da aika- aikar su a jihohi da dama na arewacin Najeriya.

Wannan karon ‘yan bindigar sun fadada ayyukan su ne na kakabawa talakawa haraji a Jihar Kebbi dake Arewa maso Yammacin kasar, wanda dole a biya ko a hadu da fushinsu.

Mako biyu da suka gabata ne mayakan Najeriya suka soma yakar ‘yan bindiga a Gabashin Sakkwato dake Arewa maso yammacin kasar duk da yake kawo yanzu babu wani bayani hukumance na nasara da aka nuna an samu sanadiyar wannan fafatawar, sai gashi kuma ‘yan bindigar sun bulla a Jihar Kebbi suna gallazawa jama'a.

Ranar Talatar makon jiya ne mahara suka afkawa wasu kauyukan yankin Ngaski dake jihar, bayan sun kwashi kayan jama'a da dabbibi, wannan mako sai suka aiko da sako kan haraji ga jama'ar kauyukan kamar yadda wani mutumin kauyen Kolo wanda ke gudun hijira a garin Yauri ya shaidawa Sashen Hausa.

Wakilin Sashen Hausa ya tuntubi rundunar 'yan sandan Najeriya akan ko suna da masaniya akan wannan batun sai dai kakakin rundunar a Jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar yace sai ya bincika. Kawo zuwa hada wannan rahoto babu wani bayani da muka samu daga wurinsa.

Da dadewa dai masharhanta akan lamurra ke bayar da shawarwari ga mahukumta akan matsalolin rashin tsaro amma dai har yanzu ba biyan bukata, abinda wasu ke ganin kamar ana yin biris ne da shawarwarin da ake bayarwa.

Wannan yankin na Jihar Kebbi dai cikin sa ne aka sace daliban makarantar sakandaren gwamnatin tarayya a birnin Yauri wadanda yanzu kusan wata bakwai sauran daliban na hannun maharan, gwamnati ta kasa ceto su duk da halin kunci da iyayen yaran suka shiga, musamman masu ‘ya’ya mata.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

A Najeriya ‘Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Daura Haraji Bayan Sun Kai Hari
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00


XS
SM
MD
LG