Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Kebbi


Yan bindiga
Yan bindiga

A Najeriya al'ummomin kasar na cigaba da fuskantar hare-haren ta'addanci daga ‘yan bindiga abinda har sun wasu daga cikinsu sun fara yanke kauna ga kawo karshen matsalolin, kawai suna jiran yadda Allah zai yi dasu.

Hakan na zuwa ne lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da haddabar al'ummomi a jihar Kebbi wadda ke arewa maso yammacin kasar suna kisa da yin garkuwa da mutane.

‘Yan Najeriya sun kasa samunkwanciyar hankali sanadiyar ayukkan ‘yan bindiga wadanda ke ci gaba da kai hare-hare babu kyakkyabtawa duk da matakan da mahukunta ke dauka don dakile ayukkan nasu.

Ranar jumu'ar makon jiya ne ‘yan bindiga suka kai zafafan hare-hare a wasu kauyukan da ke mazabar Waje da a yankin Unashi cikin karamar hukumar
Danko Wasagu a jihar Kebbi dake yammacin arewacin Najeriya inda suka hallaka mutane da dama kuma suka kama wasu ciki har da sarakuna kuma kawo yanzu babu labarin su.

Kwatsam sai gashi jumu'ar wannan mako sun sake kai hari ga wasu al'ummomi dake yankin har suka hallaka wasu daga cikin su.

Muryar Amurka ta zanta da wani mazaunin yankin wanda yace ‘yan bindiga sun mayar da yankin nasu madaddala .

Bayan harin da aka kai makon da ya gabata gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu lokacin da ya ziyarci yankin don jajantawa jama'a ya karfafa guiwar mutanen da suka yi kaura da su koma garuruwansu domin ana daukar matakan samar musu tsaro, sai dai komawar ta gagara.

Ko da Muryar Amurka ta tuntubi kantoman karamar hukumar ta Danko Wasagu, yace baya da iznin yin magana da manema labarai.

Mun kuma tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya kuma zai bincika, mu sake kiran shi bayan sa'a daya.

Sai dai daidai lokacin hada wannan rahoton, bai karba kiran ba.

Harwayau kiran mashawarcin gwamnan jihar akan lamurran tsaro Manjo Garba Rabi'u Kamba mai ritaya shima bai dauki kiran ba.

Al’ummomin dai na ci gaba da fuskantar tashin hankali da kuncin rayuwa abinda ya sa suke jaddada kiraye kiraye ga mahukumta, duk da yake mahukumtan na kan kokarin shawo kan su kuma wasu lokuta suna samun galaba amma dai matsalolin sun ki karewa.

XS
SM
MD
LG