Mahara dauke da muggan makamai ne suka afkawa wasu al'ummomi a jihar Kebbi inda suka tarwatsa jama'ar kauyukan yankin Ngaski.
Hare haren ta'addanci na ci gaba da daidaita yankunan arewacin Najeriya musamman a yammacin kasar duk da nasarar da jama'a ke hangen an soma samu ta fafatawa da mahara a gabascin Sakkwato.
Wannan karon maharan sun dira ne a wasu kauyuka na jihar Kebbi inda suka ci karen su babu babbaka.
Muryar Amurka ta zanta da wasu wanda suka tsallake fadawa tarkon maharan kuma ba su so a ambaci sunan su ba, inda su ka bayyana cewa maharan sun mammaye garin, suka tare hanya, suka dunga karban kudi, sannan suka yi ta harbe-harbe da farfasa shaguna.
Bayan wannan ta'asar hakama sai da suka kwashi shanun jama'a wadanda har yanzu ba'a san adadin su ba.
Na tuntubi rundunar 'yan sandan Najeriya akan wannan batun amma kakakin ta a jihar kebbi yace zai bincika amma dai kawo hada wannan rahoto ban ji ba daga wurinsa.
Yanzu dai babbar fargabar jama'a bata wuce rashin tabbas ba da yake ko a watanni baya da suka fara shiga yankin sun ci gaba da shiga har lokacin da suka sace daliban makarantar birnin Yauri wadanda har yanzu wasu daga cikin yaran na hannun su.
Lamarin tsaro dai a arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubale ko an fara tarbo wani wuri wani wurin sai ya rincabe, abinda ke nuna lallai sai anyi da gaske wurin magance matsalolin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: