Ministan kwadago Dokta Chris Ngige ya furta wasu kalamai da wasu ‘ya'yan kungiyar malaman jami'o'in ke fargabar suna iya mayar da hannun agogo baya ga kokarin sansantawa tsakaninsu da gwamnati.
A Najeriya fargabar jama'a kan hare haren ta'addanci na kara fadada daga yankunan karkara zuwa manyan birane, abinda masana ke cewa alama ce mai nuna matakan da mahukunta ke dauka basu iya magance matsalolin tsaro, ko a daren Asabar 'yan bindiga sun kai hari a unguwar Gagi da ke Sokoto.
A Najeriya alamu na dada nuna cewa tunkahon da gwamnatin kasar ke yi na bunkasa ciyar da kasa da abinci na dab da tashi tutar babu, saboda yadda ‘yan bindiga suke hana ayi noma a yankunan kasar.
Harin ta'addanci da aka kaiwa ayarin shugaban Najeriya na ci gaba da daukar hankalin ‘yan Najeriya musamman mazauna yankunan da rashin tsaro ya daidaita har wasu na ganin akwai ishara a ciki.
Duk da yake da yawa daga cikin gwamnatoci musamman na arewa sun yi kwaskwarima tare da saka hannu ga dokokin kare ‘yancin kananan yara, har yanzu ana samun mutanen da ke yi wa dokokin karan-tsaye suna cin zarafin yara.
Gabanin tsayuwar arfa ranar jumma'ar nan mai zuwa hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta ce alhazai dubu 25 cikin dubu 43 sun isa Saudiyya.
Jam'iyar APC mai mulki a Najeyatana ci gaba da fuskantar barazanar ficewar ‘ya'yanta zuwa wasu jam'iyu, daidai lokacin da jam'iyun ke faman samun jama'a don cin zabubukan shekara ta 2023.
Kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen duniya da suka sanya hannu ga dokar hana fatauci ko hallaka dabbobi masu fuskantar barazanar karewa a duniya, bai sa an daina hallaka irin wadannan dabbobin ba a cikin kasar.
An tabbatar da mutuwar jami'an ‘yan sandan mopol shida, a wani kwanton bauna da ‘yan bindiga suka yi musu a jihar Sokoto.
Wadansu maniyata daga jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya sun hadu da tsautsayi akan hanyar su daga Isa zuwa Sakkwato inda zasu jirgi zuwa saudi Arabia.
Cibiyar fafatukar wanzar da zaman lafiya ta kasar Amurka ta himmantu wajen karfafa gwiwar wanzar da zaman lafiya a Najeriya yayinda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da haddabar jama'ar kasar.
Yau aka cika shekara daya cif da sace daliban makarantar sakandaren Birnin Yauri dake jihar Kebbi inda har yanzu maharan ke rike da dalibai goma sha daya mata.
Wadansu ‘yan gudun hijira a Najeriya sun yi dace ta wajen samun tallafin gidaje kyauta daga al'ummomin kasar Qatar a daidai lokacin da dubban ‘yan gudun hijira ke zama a matsugunan wucin gadi marasa inganci.
A Najeriya masana lamurran tsaro na ganin rashin daukar shawarwari da ake bayarwa ga gwamnati ba daga cikin abubuwan da suka sa aka kasa kawo karshen matsalolin rashin tsaro dake addabar kasar.
A Najeriya yayin da jam'iyyun siyasa suka ja daga da hanyar tsayar da ‘yan takara domin fafatawa a zabubukan shekara ta 2023, babbar jam'iyar adawa ta PDP na ci gaba da kara samun karfi a wasu Jihohin kasar.
A Najeriya daidai lokacin da jama'a ke ci gaba da alhinin kisan gilla da aka yiwa masu ibadah a jihar Ondo, muhimman mutane na ci gaba da yin Allah wadai da wannan kisan, da kuma kira ga Kirista a kan kar su dau doka da hannu.
A Najeriya masana na ganin sakaci da rikon sakainar kashi ga gwamnati ke yi wa bangaren ilimi shi ke sa ‘yan kasar fita kasashen waje neman ilimi. Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ce-ce-ku-ce tsakanin gwamnatin jihar Sokoto da wani dalibi dan asalin jihar mai karatu a kasar Rasha.
A Najeriya korafe-korafe bayan zabuka abu ne da ya zamo ruwan dare, kuma yake ci gaba da wanzuwa duk da illolin da hakan ke haifarwa ga jam'iyun siyasa da ma tsarin dimokradiyya.
A Najeriya alamu na nuna irin rashin tabbas da ake samu tsakanin ‘yan siyasa duk da kokarin da ake yi na sasanta bangarori da ke rikicin cikin gida a jam'iyyun.
A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya jam'iyyar ta gudanar da zaben tsayar da dan takarar ta ta hanyar sasanci wanda gwamna Tambuwal ya jagoranta.
Domin Kari