Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Sun Ba ‘Yan Gudun Hijira Tallafin Gidaje 150


Gidajen da Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya su ka ginawa ‘Yan Gudun Hijira a jihar Sokoto
Gidajen da Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya su ka ginawa ‘Yan Gudun Hijira a jihar Sokoto

Wadansu ‘yan gudun hijira a Najeriya sun yi dace ta wajen samun tallafin gidaje kyauta daga al'ummomin kasar Qatar a daidai lokacin da dubban ‘yan gudun hijira ke zama a matsugunan wucin gadi marasa inganci.

SOKOTO, NIGERIA - 'Yan gudun hijira da ke jihar Sakkwato, arewa maso yammacin Najeriya, wadanda ke zaune a wasu al'ummomi dake garin Tabanni a yankin Ghandi ta Rabah da harin ‘yan bindiga ya tarwatsa fiye da shekara 4 da suka gabata, sun yi dace da samun taimako daga kungiyar ayukkan agaji ta Qatar ta hannun hukumar zakka da wakafi, wadda ta gina musu gidaje na zamani har 150, da masallatai da assibiti da rijiyojin burtsatse da dai sauran abubuwan bukatar zaman al'umma ga wuri.

Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Sun Bada Tallafin Gidaje 150 Kyauta Wa ‘Yan Gudun Hijira
Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Sun Bada Tallafin Gidaje 150 Kyauta Wa ‘Yan Gudun Hijira

A hirar shi da Muryar Amurka, daraktan cibiyar ta Qatar Sheikh Hamdi Abdu ya ce sun yi wannan aikin domin ya amfani jama'a.

Yana mai cewa, “Da yardar Allah duk mutanen wurin zasu amfana da ilimi da lafiya da duk fannonin da cibiyar ta agaza, Alhamdulillah kowa ya ga yadda irin amfanin da muka samar na taimakawa jama'a, kuma muna bukatar gwamnatin jiha ta shirya wa yara dubu daya karatu mu dauki nauyin karatun su"

Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Sun Bada Tallafin Gidaje 150 Kyauta Wa ‘Yan Gudun Hijira
Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Sun Bada Tallafin Gidaje 150 Kyauta Wa ‘Yan Gudun Hijira

Gwamnatin Sakkwato dai ita ce ta baiwa cibiyar filin da ta gudanar da wannan aikin na taimako ga wadanda ibtila'i ya shafa, a cewar mataimakin gwamna Manir Muhammad Dan'iya.

Wannan cibiyar ta jima tana gunadar da ayukkan jinkai a Najeriya da kasashen duniya daban-daban.

Wasu masana da Muryar Amurka ta yi hira da su sun kalubalanci ‘yan Najeriya dake zaune tare da ‘yan gudun hijirar su yi koyi da wannan karamcin domin kawar da damuwa da halin kunci da wadansu 'yan gudun hijiran kan shiga.

Yanzu haka akwai dubban ‘yan gudun hijira wadanda tashe-tashen hankula suka raba da gidajensu a sassa daban daban na arewacin Najeriya wadanda akasarin su su ke cikin halin damuwa kamar wadansu da ke zaune a wani kangon gida da Muryar Amurka ta yi hira da su.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Al’ummomin Kasar Qatar A Najeriya Sun Bada Tallafin Gidaje 150 Kyauta Wa ‘Yan Gudun Hijira
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG