Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Fataucin Dabbobi Masu Fuskantar Barazanar Karewa A Duniya


Dabbobi Masu Fuskantar Barazanar Karewa A Duniya
Dabbobi Masu Fuskantar Barazanar Karewa A Duniya

Kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen duniya da suka sanya hannu ga dokar hana fatauci ko hallaka dabbobi masu fuskantar barazanar karewa a duniya, bai sa an daina hallaka irin wadannan dabbobin ba a cikin kasar.

Abin da ke nuna hakan shine yadda ake kama jama'a da wani abu mai nuna an hallaka nau'in dabbobin, kamar yadda aka kama fatun jakkai fiye da dubu biyu a jihar kebbi dake arewa maso yammacin kasar.

Dabbobi Masu Fuskantar Barazanar Karewa A Duniya
Dabbobi Masu Fuskantar Barazanar Karewa A Duniya

Yanzu bai kai wata uku ba da aka kama wasu mutane da safarar naman jakuna fiye da dubu daya a jihar kebbi, suna yunkurin fita da shi, abin da ya sabawa wasu sassa na dokokin Najeriya, sai gashi an sake kama fatun jakuna fiye da dubu biyu a jihar a cewar Kontorolan hukumar hana fasa kwabri a jihar Joseph Attah.

Wannan lamarin yana faruwa ne duk da kasancewar Najeriya daya daga cikin kasashen duniya da suka amince da hana fatauci ko kisan dabbobi masu fuskantar barazanar karewa bisa doron kasa da suka hada da jakuna.

Hukumar ta hana fasa kwabri ta hannunta fatun jakunan ga hukumar kulawa da shige da ficen nau’o’in kebantattun dabbobi da kayan amfanin gona, wadda wakilin ta Mr Idris Dakat ya ce ba wannan ne karon farko ba, da ake kama irin wadannan fatun jakunan a Najeriya.

Masu sharhi akan lamurran yau da kullum irin farfesa Tukur Muhammad Baba na ganin cewa a Najeriya ba sa hannu ga yarjejeniya ne ke da wuya ba, aiwatar da cika yarjejeniyar.

Hakama masana na ganin ilmantar da ‘yan kasa akan muhimmancin kasa da shiga cikin kasashen duniya ga saka hannu kan wani al'amari zai taimaka wajen rage wadannan matsalolin.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

XS
SM
MD
LG