Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole A Daina Saka Siyasa Cikin Sha'anin Samar Da Tsaro - Tambuwal


Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Harin ta'addanci da aka kaiwa ayarin shugaban Najeriya na ci gaba da daukar hankalin ‘yan Najeriya musamman mazauna yankunan da rashin tsaro ya daidaita har wasu na ganin akwai ishara a ciki.

Yanzu haka dai wasu al'ummomi da ke fama da matsalar tsaro har sun gwammace da ma ace ba ‘yan Najeriya ba ne.

‘Yan Najeriya musamman na yankin arewa sun jima suna kokawa akan matsalolin rashin tsaro dake son ganin baya ga resu a sassa daban daban.

Al'ummomi a gabashin Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya sun jima cikin halin kunci akan ayukkan ‘yan bindiga kuma har yanzu ba wata mafita duk da koken da suke yi ga mahukunta.

Wannan ne ma ya sa harin da aka kaiwa ayarin shugaban Najeriya a jihar Katsina wasu ke ganin akwai abin ishara a ciki.

Aminu Almustapha Boza dan majalisar jiha ne wanda ya jima yana fafatuka akan matsalolin rashin tsaro a gabascin Sakkwato. Ya kuma ce maganar da yayi shekura biyar da suka wuce ya tabbata, ga shi yau an wayi gari ana tare ayarin gwamnoni da na shuwagabanin kasa.

Shi ma Gwamnan Aminu Waziri Tambuwal ganin ya ke yi akwai bukatar kara yiwa kasa addu'a da kuma fuskantar matsalolin da gaske.

“Abu ne da ke nuna akwai bukatar kara zage damtse ga yin addu'o'i, a kuma hada kai wuri daya a tunkari matsalar kuma dole a daina saka siyasa cikin sha'anin samar da tsaro, abu ne da ya shafi kowa ba wai shugaban kasa kadai ba ko kuma Muhammad Buhari zaman sa mutum ko Aminu Waziri Tambuwal a zaman gwamnan Sakkwato “

Duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sandan Najeriya yayin rubuta wannan rahoton, akan hare haren da mazauna yankunan gabashin Sakkwato ke fuskanta ya ci tura.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG