Masana lamurran siyasa na ganin akwai wadansu abubuwa wadanda muddin ba'a kula da su ba, ba za'a daina samun irin wadannan matsalolin ba.
Zabubuka a kasashe masu tasowa kamar Najeriya sau da yawa sukan ci karo da korafe-korafe bayan zabe musamman daga wadanda ba su samu galaba ba a zabubukan.
Haka kuma daga zabukan shugabancin jam'iyu ko na fitar da ‘yan takara koma manyan zabuka, kamar wannan korafi da wakilan kungiyoyin jam'iyar APC suka gabatar a Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya bayan zaben fitar da dan takarar gwamna.
Wasu lokuta ma tun kafin gudanar da zabuka wasu sukan gabatar da korafi musamman idan suna hangen za'a yi masu ba daidai ba, ko kuma suna ganin za su sha kasa a zabe, kamar yadda wasu daga cikin masu neman takarar gwamna a jam'iyar suka gabatar kafin zaben fitar da dan takarar Sokoto.
Ita kuwa jam'iya bayanin da ta fitar bayan zaben ya nuna an gudanar da zabukan bisa tsarin doka.
Masana sun bayyana cewa wadannan matsalolin suna illoli, domin sukan kawo rauni ga tsarin mulkin dimokradiya.
Farfesa Tanko Yahaya Baba, na sashen nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto ya ce abin da ke sa ana kwan-gaba-kwan-baya a harkar zabubukan Najeriya shi ne raunin da ake samu wajen hukumta wadanda suka saba dokokin zabe.
Kungiyoyin fafatuka ma suna gudunmuwar da ya kamata su bayar wajen daidaita tsarin zabubuka.
Sai dai wata matsala dake tattare ga kungiyoyin fafatuka ita ce akasarin su, sun fada hannun ‘yan siyasa sai yadda suke so suke yi da su, abin da ya sa tasirinsu ya raunana, kuma korafe-korafe suka yawaita.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: