Cibiyar dai tana hada hannu ne da jami'o'in kasar don samun nasarar aikin ta.
Zaman lafiya da kwanciyar hankali har yanzu sun gagari wasu al'ummomi a Najeriya kuma babban yunkuri da mahukunta ke yi wajen samar da zama lafiya bai wuce amfani da jami'an tsaro ba.
Sai dai masana na ganin karfin soji ko sauran jami'an tsaro kadai yana wuya ya samar da zaman lafiya mai dorewa, saboda akwai wasu kananan abubuwa da tun farko sune ke haifar da tashin tashina har akai ga tashin hankali, wadanda dole sai an magance su.
Kan hakan ne Cibiyar wanzar da zaman lafiya ta kasar Amurka ke hada hannu da jami'o'i da masu ruwa da tsaki a Jihohin Najeriya domin samar da kungiyoyi da zasu yi aiki domin samarda zaman lafiya a cikin al'umma.
A hirar shi da Muryar Amurka, Ambasada Zango Abdu jami'in gudanarwa na cibiyar a Najeriya yace suna son jawo hankalin gwamnati da mutane don ciyar da akidar zaman lafiya gaba.
Cibiyar wadda ke zagaye sassa daban daban na kasar tace ta fara ganin haske ga fafatukar da take yi musamman a yankin arewa maso gabascin Najeriya.
General Martin Luther Agwai mai ritaya yana cikin jakadun da ke gaba-gaba wajen samar da zaman lafiya a cikin al'umma, yace aikinsu shine su baiwa gwamnati shawara akan abubuwan da ita kanta tana hango wasu daga cikinsu.
“Zamu ci gaba da bayar da shawarwari ga gwamnati akan yadda za'a samu ci gaba, kuma muna fatar aiwatar da su, ta amfani da abinda ke hannun gwamnati, da kuma azamar ta don kare kasar nan ta zauna lafiya.
Mai sharhi akan lamurran yau da kullum Farfesa Tukur Muhammad Baba wanda ya taba zama darakta a cibiyar wanzar da zaman lafiya ta jama'ar Usmanu Danfodiyo wadda da hadin guiwarta ne cibiyar ta kasar Amurka ta shigo yankin arewa maso yamma yace akwai fata, a cikin wannan yunkurin.
Babbar fata dai ba zata wuce samun nasara ba ga dukan kokarin da ake yi domin wanzar da zaman lafiyar al'umma.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: