Lokacin da Muryar Amurka ta zanta da shugaban karamar hukumar ta Isa, Abubakar Yusuf Dan Ali yana tare da gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal wanda ya tabbatar da lamarin da ya shafi maniyya 21.
Wani bayani da muka samu daga majiya mai tushe daga asibitin Isa ta ce ‘yan bindigar sun harbe jami'an mopol 3.
Muryar Amurka ta kuma tuntubi rundunar 'yan sandan domin neman tabbacin wannan batun amma abin ya ci tura.
Bayan shekaru biyu masu son yin aikin Hajji daga kasashen duniya basu samu damar yinsa ba saboda lalurar cutar korona birus, wannan shekarar maniyata sun kasance cikin farin ciki samun wannan damar inda yanzu haka dubban mahajjata daga kasashen duniya sun Isa kasa mai tsarki.
A jihar kebbi ma dake makwabtaka da jihar Sakkwaton jama'a ne ke ta kokawa akan matsalolin rashin tsaro dake hana su shiga gonakkin su, kuma ga Damina ta kama.
Wani mazaunin garin Bena Malam Salihu yace idan zasu je gona dole sai sun dauki masu iya basu kariya kada ‘yan bindiga su mamaye su lokacin da suke aiki.
Wadannan matsalolin na faruwa ne duk da yake mahukunta na kokarin tura jami'an tsaro a yankunan, abinda jama'ar wuraren ke kara kira akan samun Karin dauki don magance matsalolin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: