Wannan na zuwa ne lokacin da jami’an tsaro ke ta kokarin kama masu aikata ta'addanci, kuma ta’addancin ya ki raguwa.
Sau da yawa gwamnatin Najeriya ke cewa tana iya kokarinta wajen magance matsalar rashin tsaro, kuma wasu lokuta akan samu rahotanni na ko dai an fafata tsakanin tsaro da ‘yan ta'adda ko kuma an kame ‘yan ta'addar amma kuma matsalar taki karewa.
A jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar, jami'an tsaro sun jima suna kama ‘yan bindiga, inda ko a wannan mako jami'an tsaron ‘yan kasa na Civil Defence sun kama masu garkuwa da mutane su hudu a cewar kwamandan rundunar Muhammad Sale Dada. Mutanen da aka kama sun kuma aminta da laifin da ake tuhumar su akai.
Sai dai ra'ayin masana lamurran tsaro ya sha bamban dana jami'an tsaro, domin acewar shugaban sashen nazarin aikata laifuka da tsaro na jami'ar Yusuf Maitama Sule dake Kano, detective Auwal Bala Durumin iya muddin gwamnati bata daukar shawara yana wuya a iya kawo karshen wannan matsalar.
Wasu kuma na ganin rashin hukumta wadanda ake kamawa bainar jama'a na daga cikin abubuwan da ke sa matsalar taki karewa.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: