Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Musulmi Ya Jajanta Wa CAN Kan Harin Owo


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

A Najeriya daidai lokacin da jama'a ke ci gaba da alhinin kisan gilla da aka yiwa masu ibadah a jihar Ondo, muhimman mutane na ci gaba da yin Allah wadai da wannan kisan, da kuma kira ga Kirista a kan kar su dau doka da hannu.

Majalisar koli a kan lamurran addinin Musulunci a Najeriya karkashin jagorancin Mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad na daga cikin jerin wadanda suka yi tir da wannan aika-aikar.

Tun daga ranar Lahadin wannan mako da al'amarin ya faru wanda ya yi sanadin salwantar rayuka masu tarin yawa jama'a da kungiyoyi ke nuna alhini a kan wannan aikin na rashin tausayi.

Majalisar koli a kan lamurran addinin Musulunci a Najeriya karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi a wani bayani da daraktan mulkin ta Zubairu Haruna Usman Ugwu ya fitar wanda wasu jaridu suka wallafa, Mai alfarma sarkin Musulmi ya bayyana wannan aika-aikar da cewa yin ta'addanci ne ga ruhin bil'adama kuma babban laifi ne.

Shugaban majalisar kolin ya bukaci gwamnati da ta baiwa jami'an tsaro wa'adin da za su gudanar da bincike tare da zakulowa da hukunta wadanda suka yi wannan mummunan aikin wanda bai tsayu ga keta alfarmar rayuwar bil'adama kadai ba har ma da addini.

Ya ce Majalisar tana nuna alhininta ga kungiyar Kiristoci ta Najeriya, da mabiya darikar Catholic, da gwamnatin jihar Ondo, tare kuma da yin ta'aziya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa da addu’ar samun zaman lafiya da wanzuwar tsaro a cikin Najeriya.

Harilayau muhimman jama'a na ci gaba da nuna alhinin su akan wannan lamarin abinda ya sa na tuntubi shugaban kungiyar mabiya addinin Kirista a Sakkwato Reverend Father Nuhu Iliya a kan wannan batun.

Reverend Father Nuhu Iliya ya yi kira ga shugabanni da su tashi tsaye a kan aikin sun a kiyaye rayuwar al’umma da dukiyoyin su.

Rahotannin sun nuna cewa tuni mahukumta suka kaddamar da bincike a kan wannan mummunan hari da aka kai a wannan mujami'a ya yin da wadanda suka samu raunuka ke ci gaba da samun kulawa.

Wannan lamarin ya faru ne lokacin da gwamnatin Najeriya ta jima tana cewa tana kokarin samar da tsaro da kare rayukan ‘yan kasa inda har shugaban kasar ya sha alwashin kawar da ayukkan ta'addanci kafin karewar wa'adin Mulkin sa wanda yanzu yana kasa da shekara daya, abin da wasu jama'a ke ganin cewa gwamnati ba da baske take ba.

Daga Sokoto ga rahoton Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yaki Da Matsalar Almajiranci A Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG