Shugaban zai gabatar da kasafin kudin na 2023 a gaban Majalisar Dokokin kasar, wanda zai kai Naira triliyan 19.7, hakan na nufin an samu karin Naira triliyan 2 tsakani da kasafin kudin bana da zai kammala a watan Disamba.
A Najeriya, Hukumar Wayar da kan Al'umma da hadin gwiwar Ma'aikatar Kula da ayyuka na musamman sun kaddamar da wata kungiya wacce za ta aiwatar da kudurin mata a fanoni daban daban, kama daga Siyasa, zaman lafiya da tabbatar da dogaro da kansu.
Majalisar dattawa Najeriya ta kasa daukar matsaya kan wa'adin makwanni 6 da ta bai wa Shugaba Mohammadu Buhari kan ya dauki kwararan matakai akan sha'anin tsaro ko kuma ta tsige shi, a maimakon haka ta mayar da hankali ne akan shirin kasafin kudin badi.
Majalisar zartarwa ta Najeriya ta amince da kashe Naira Miliyan 718 don ayyukan tsaro da sa ido kan harkokin sufurin jiragen kasa na Abuja.
Da alamar dai har yanzu matsalar nan ta rashin bin ka'ida da kuma tsautsayi na ci gaba da addabar bangaren gine gine a Najeriya, inda aka sake gamuwa da hadarin faduwar gini a Abuja, inda wasu mutane su ka mutu, wasu kuma su ka ji raunuka.
Daga dukkan alamu an sami rudani a kan yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ke kashe kudade kan tallafin man-fetur, har ya sa Majalisar Wakilai kafa Kwamitin wucin gadi domin ya yi bincike a kai.
Yayin da kowane bangare ke kokarin sauke nauyi wajen ganin an samu tsaro a Najeriya, Majalisar Dattawa ta bai wa shugabannin bangaren tsaro wa'adin makwanni hudu su tabbatar an tsaro tsao a kasar ko kuma ta dau mataki na gaba.
Hukumar Alhazan Najeriya ta bada hakuri ga wadanda ba su samu yin aikin Hajji bana ba, tare da shan alwashin za ta yi bincike ta hukunta wadanda suka jawo wa alhazan jinkiri idan an tabbatar da laifi akan su.
Musulmin Duniya million daya a ciki har da na Najeriya dubu 43,008 ne suke hawan dutsen Arafa a Yau Jumma'a .
Hukumomin Saudiya sun kara wa Najeriya kwana guda domin bada dama ga masu niyyar aikin hajji bana su iya gudanarwa, biyo bayan gaza kwashe alhazan a kan lokaci da jiragen jigila su ka yi.
Batun tikitin takarar Musulmi da Musulmi na ci gaba da daukan hankali a Najeriya musammana a Arewacin kasar inda kungiyoyin addini ke cewa ba shi ne mafita ba.
Kwararru a harkar man fetur suna ta mahawara akan yiwuwar magance karancin man fetur dake addabar kasar a yanzu, a yayin da suke ganin ya samo asali ne daga yakin da ake tafkawa tsakanin kasar Rasha da Ukraine.
Masana harkokin Shari'a da masu yin nazarin Kundin Tsarin Mulkin kasa na sharhi akan sauya sunayen yan takara wadanda ba su kasance a zaben fidda gwani a mazabun su ba. Inda suka nuna cewa sabuwar dokar zabe ta haramta yin haka.
Domin Kari