Kwararru masu nazari a fannin tsaro na tafka mahawara a kan wa'adin makwanni hudu da Majalisar Dattawa ta ba wa shugabanin hukumin tsaro domin su Kawo karshen rashin tsaron da ke addabar kasar inda wasu ke ganin an bar gini tun rani, wasu kuma na cewa an mayar da harkar tsaron kasuwanci ne kawai.
A cikin shekarun nan bakwai da wanan Gwamnati ta hau karagar mulki, Majalisar Dattawa ta yi mahawara tare da tsokaci akan rashin tsaro sama da sau 45 akan, amma a kullum kamar kara lalacewa lamarin ke yi. A wannan karon ma Majalisar ta yi wata ganawa ta sa'o'i biyar da shugabanin tsaron kasar, har sai da aka kai ga ba su wa'adin makwanni hudu domin su kawo karshen rashin tsaro da ke addabar kasar.
Sanata Abdullahi Ibrahim Danbaba wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin yan sanda ya ce dole ce ta sa Majalisar ta gayyato jami'an tsaron domin halin rashin tsaron kasar ya tsorata su kuma suna so su ga an samu sauyi nan ba da jimawa ba.
Ganin cewa an jima ana irin wannan ganawar amma lamarin sai kara rincabewa ya ke yi, ya sa mai fashin baki a al'amuran tsaro Keftin Aliyu Umar Babangida yin tsokaci da kakkausar murya, ya na mai kiran da a gaggauta zage dantse saboda munin al'amarin.
Shi ma mai nazari kan al'amuran tsaro da zamantakewa, Abubakar Aliyu Umar, ya yi jawabi cikin fushi ya na cewa wasu na samun kudi ne da harkar tsaro shi ya sa ma batun shawo kan rashin tsaron ke tafiyar hawainiya duk kuwa da rashe rashen rayukan da ake ta yi.
To saidai Sanata Abdullahi Ibrahim Danbaba ya bada tabbacin cewa a wannan karon akwai alamun za a samu sauyi domin sun gamsu da bayanin jamián tsaron.
Abin jira a gani shi ne irin matakan da jami'an tsaron za su dauka da zai kawo sauyi a lamarin tsaron cikin gaggawa.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda: