Wanan magana ta samo asali ne daga matsalolin da suka shafi aikin Hajjin na bana, ganin cewa akwai wasu maniyata 1901 daga cikin alhazai 43,008 da ba a iya kwaso su zuwa kasa mai tsarkin domin sauke faralin su ba.
Kwamishina Mai kula da Ma'aikata da hadahadar kudi na Hukumar Alhazai ta kasa, Nura Hassan Yakasai ya yi karin haske akan wannan batun. Yana mai cewa basu ji dadin yadda aka samu tangarda a cikin lamarin ba kuma su ma suna taya su bakin ciki.
Akwai wani zargi da aka yi ta yayatawa ta faifan bidiyo a dandalin sada zumunta cewa akwai wadansu ma'aikatan hukumar da suka rika karban kudin maniyata akan wai za a samar masu jirgi na musamman da zai kwashe su zuwa kasa mai tsarki. Akan haka, Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa Zikirullahi Kunle Hassan ya ce lallai hukumar za ta yi bincike kuma za ta dauki matakin hukunci idan an tabbatar da laifi akan kowane jami'in ta.
A nan Zikirullahi ya jadadda cewa Hukumar alhazai za ta yi bincike akan wannan zargi har in ya kama ma za ta hada gwiwa da Hukumar EFCC domin tabbatar da sahihancin wannan labarin, saboda ba aikin hukumar alhazai ba ne karban kudi a hannun maniyata.
Zikirullahi ya ce in an tabbatar da laifi, za a hukunta wadanda abin ya shafa.
A halin yanzu alhazan duniya sun kammala aikin hajjin , tare da barin tantunan su na Muna zuwa garin Makkah inda za su cigaba da ibada kafin su koma kasashen su.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: