Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudi Na Karshe A Gaban Majalisar Dokoki


Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban zai gabatar da kasafin kudin na 2023 a gaban Majalisar Dokokin kasar, wanda zai kai Naira triliyan 19.7, hakan na nufin an samu karin Naira triliyan 2 tsakani da kasafin kudin bana da zai kammala a watan Disamba.

ABUJA, NIGERIA - Wannan Kasafi shi ne na karshe da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari zai gabatar kafin wa'ádin mulkinsa da zai kare a watan Mayu na shekara ta 2023.

Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))
Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

A dogaro da hasashe na kasafin kudin na shekara 2023, an kiyasta ma'aunin gangar man fetur a kan dallar Amurka 70 sabanin dallar Amurka 65 da aka kiyasta a kasafin wannan shekara da mu ke ciki.

A wannan kasafin za a samar da danyen man fetur ganga miliyan 1.67 ko wacce rana a kan chanjin farashin dallar Amurka daya a Naira 435.57

An yi hasashen gibi zai kai Naira triliyan 12.41 a shekara 2023, wanda ya nuna sama da Naira tiriliyan 7.35 da aka yi kasafin wannan shekara da muke ciki, wanda ke nuna kashi 196 na jimlar kudaden shiga, ko kuma kashi 5.50 na ma'aunin karfin arzikin kasa wato GDP.

Naira
Naira

Idan za a samu gibi har na Naira triliyan 12.41, hakan na nufin sai an kara ciwo bashi kafin a aiwatar da kasafin kudin?

Masanin Tattalin arziki Sa'ad Usman, ya ce, mutane suna da gaskiya idan suna korafi cewa ana ciwo bashi da yawa a kasar, ko da yake, in da za a ga ayyukan da ake yi da kudaden ba za a damu ba.

Sa'ád ya kara da cewa, kasashe da dama na ciwo bashi domin yin ayyukan ci gaba a ciki har da Najeriya.

Abin lura shi ne, so tarin ana samun yawan korafi a kan yanayin talauci da kasa ke ciki duk da bayanan cewa kasafin zai dau matakan kyautata sassan tattalin arziki da zai shafi jama’a kai tsaye.

Masanin tattalin arziki Shu’aibu Idris Mikati, ya ce hakika kasafin ba ya nuna tasiri na zahiri a kan talakawa da su ne akasarin al’ummar Najeriya saboda wasu ba sa samun abinci sau uku a rana, wasu sau daya kawai suke samu su ci. Mikati ya ce dayawan mutane suna karban kasa da kwatankwacin dallar Amurka daya ko wacce rana a wuraren aiki,saboda haka kudin ba ya isan su.

Mikati ya lura da wani kalubale na kara yawan kasafin wasu daga ma’aikatu da majalisa kan yi, don la’akari da bukatar ta su ta haura yadda su ka nema; alhali rinjayen kasafin sai an ciwo bashi wajen aiwatar da shi, wani abu da har ya sa ake zargin yan majalisa da yin chushe a kasafin kudi duk shekara.

Shugaba Buhari ya dau salon yin kasafi daga watan Janairu ya kare a watan disamba, wanda bambancin kawai na zahiri da a ke gani, tsakanin Gwamnatinsa da sauran gwamnatoci, shi ne abin da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ke cewa , gwamnatin ta APC ta na samun nasarar aiwatar da mafi yawa, daga abin da ke cikin kasafin da ta kan gabatar a duk shekara.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Buhari Zai Gabatar Da Kasafin Kudi Na Karshe A Gaban Majalisar Dokoki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

XS
SM
MD
LG