Hawan dutsen Arafa yana daya daga cikin rukunan addinin Musulunci wanda shi ne ke tabbatar wa Musulmi da sunan wanda ya sauke farali wato ya yi aikin Hajji.
Manyan Malaman addini irin su Sheikh Ahmed Suleiman Ibrahim sun gargadi Musulmi da su kaurace wa yin amfani da wayoyin su na salula--wato yar yawo saboda su natsu wajen yin addu'o'in a wannan rana mafi girman daraja.
Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta tattauna da Malamin da ke gudanar da aikin Hajji a Makkah, a kan muhimmancin hawan Arafa.
Saurari bayanin Sheikh Ahmed: