A daidai lokacin da rashin tsaro ke ci gaba addabar harkokin sufuri a fadin Najeriya, yanzu haka an mika kwangilar samar da tsaron tashar jirgin kasa ta Abuja ga kamfanoni masu zaman kansu.
To sai dai kwararru a fannin tsaro sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan wannan mataki, yayin da wasu ke ganin ya kamata a fara ta tunkarar ‘yan ta’addan dake dasa ababen fashewa, kafin a samar da tsaro ga tashar jirgin kasa.
Babban sakataren yada labarai na ma'aikatar birnin Tarrayya, Anthony Ogunleye ya sa hannu shine ya sanya hannu kan wata takardar kwangilolin da za su shafi samar da aiyukan tsaro ga tashar jirgin kasa ta Abuja, da ababen more rayuwa na cibiyar sadarwa da kuma na'urorin lantarki, har ta tsawon shekaru biyu.
Masanin harkokin tsaro Kaftin Aliyu Umar Babangida, na ganin wannan aiki da ake kokarin samarwa akwai alamar lauje cikin nadi, domin idan an samar da wannan aiki a birnin tarayya sauran manyan biranen kasar da rashin tsaro ke addaba ya za a yi da su.
Haka kuma, ganin yadda jami’an tsaron kasar suka kasa cimma burin samar da zaman lafiya, ta wacce hanya kamfanonin tsaro masu zaman kansu za su iya hakan.
Domin jin ra’ayoyin masana tsaro saurari rahotan Medina Dauda.