Hukumar Alhazan Najeriya ta fitar da sanarwar fara jigilar Alhazan Najeriya ranar 9 ga wanan wata a daidai lokacin da ta rattaba hannu a yarjejeniyar jigilar tare da wasu kamfanoni jiragen sama guda uku a ciki har da Kamfanin Kasar Saudi Arabia.
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya shirya wani taro na shugabanin majalisun dokokin kasashen Afrika da zummar neman hanyar samar wa nahiyar sauki musamman a bangaren tattalin arziki ta hanyar yin magana da murya daya.
Kamfanonin sadarwa a Najeriya suna neman a kara kudin yin waya da kashi 40 cikin 100 sakamakon tashin farashin gudanar da kasuwanci a kasar da su ka ce ana fuskanta.
Majalisar Dattawan Najeriya tana mataki na karshe a gyara dokar ta'addanci ta shekara 2013 wadda za ta haramta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane.
Akwai tabbacin za a yi aikin Hajji bana bayan an yi shekaru biyu ba a yi ba saboda bullar cutar corona da ta karade duniya.
Ya zuwa lokacin daukan wannan rahoto, Ministoci biyu ne suka baYyana aniyar tsayawa takarar kujerar Shugaban kasa a zaben shekara 2023.
Shugaba Mohammadu Buhari ya ce yana goyon bayan hukuncin wata kotun tarrayya da ke Abuja a karkashin mai shari'a Donatus Okoronkwo da ta ce a ba mata kashi 35 cikin 100 Na mukamai ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya kafa wani kwamitin wucin gadi na mutum bakwai a karkashin mataimakin mai tsawatarwa Aliyu Sabi Abdullahi da zai binciki karin kudin fito da masu kamfanonin hadahadar shirye shiryen talabijin da ke aiki a kasar suka bullo da shi.
Kungiyar Taraiyyar Turai ta zo kwarya a hannu tana neman kara karfafa dangantakar ta da Najeriya musamman a fannin samar da iskar gas zuwa kasashen Turai sakamakon yakin da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine.
Majalisar Dokokin Najeriya ta jaddada kokarinta na hana yaduwar makamai domin dakile duk wani yunkuri na ta'addanci baki daya a kasar.
Ma'aikatar Jinkai da Walwalar Jama'a ta ce daga watan Yuni na wannan shekara, za ta kammala wani tsari na tallafawa masu karamin karfi wadanda ake baiwa dubu biyar duk wata, don rage radadin talauci.
Batun rashin tsaro da ya kara ta'azzara a kasa ya sa an yi mahawara mai zafi a majalisar wakilai, yayinda wasu ‘yan majalisar suka nemi a rufe majalisar dokokin kasar.
Takkadama ce ta kunno kai a Majalisar Dattawa kan batun daukaka kara da majalisar dokoki kasar ta ce za ta yi, a game da hukuncin cire sashe na 84 karamin sashe na 12 daga sabuwar dokar zabe ta shekara 2022.
A karo na biyu cikin watanni biyu da rabi , an samu rugujewar cibiyar wutar lantarki ta kasa a Najeriya, lamarin da ya jefa jihohi bakwai da babban Birnin Tarayya Abuja cikin duhu.
Shugaba Mohammadu Buhari da yake ziyara a Ingila, yayi Allah wadai da rigingimun da ke faruwa a jamiyyar APC mai mulki, musamman ma batun shugabancin Jamiyyar. Wannan bayani ya fito ne a wata takarda ta musamman da Garba Shehu ya sanyawa hannu.
Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Sanata Yahaya Abdullahi Abubakar tare da dukkan ‘ya’yan jamiyyar su 70, sun a nuna cewa sarkin yawa ya fi sarkin karfi.
Domin Kari