Kiddiga ta nuna cewa, kashi 72 cikin 100 na yan Majalisar kasa ne suka fadi a zabukan fid da gwani a mazabun su ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, da tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio, da Shugagaban masu rinjaye Yahaya Abdullahi Abubakar da tsohon gwamnan jihar Kebbi Adamu Aliero.
Ko da yake Ahmed Lawan da Godswill Akpabio sun samu sa'a Jamiyyar APC ta mika sunayen su ga Hukumar zabe a matsayin 'yan takara duk da ba a yi zaben fidda gwani da su a mazabun su ba.
Jamiyyar APC ta bada sunan Ahmed Lawan a maimakon Sunan Bashir Sherif Machina wanda shi ne wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani a Jihar Yobe ta Arewa, shi ma tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio shi ne aka mika sunan sa ga hukumar zabe maimakon Udom Ekpoudom wanda shi ne ya ci zaben fidda dan takara a shiyar Arewa ta Yamma a Jihar Akwa Ibom .
Kwararre a harkar Shari'a Barista Mainasara Ibrahim Umar ya ce Ahmad Lawan baya cikin wadanda suka shiga cikin waccen takara suka fafata, har wancen ya sami tikiti, saboda haka haramu ne a dokar Najeriya ya ce zai iya fitowa koda ace za a sake wannan, ace za a kuma yi da shi.
Ko da yake, kwqmishinan watsa labarai na hukumar zabe Festus Okoye ya bayyana wa gidan telebijin na Arise cewa Hukumar Zabe ba ta da hurumin kin karban sunayen da jamiyyu suka aika mata, tunda jammiyyu sune doka ta ba su dama su gudanar da zabukan fidda gwani, ita Hukumar Zabe aikin ta shi ne sa ido domin ta tabbatar an bi dokoki wajen yin zaben, daga bisani sai ta fitar da rahoto.
Okoye ya ce dan takara yana iya neman izinin yin amfani da rahoton hukumar zabe idan bai gamsu da matakin da Jamiyyar sa ta dauka ba.
Akan haka ne muryar Amurka ta tuntubi Hussaini Mohammed Isa, mai magana da yawun Bashir Sheriff Machina wanda shi ne ya lashe zaben fidda gwani a Yobe ta Arewa, inda ya ce yanzu dai haka suna cikin shirin kai kara kotu don sauyen da aka yi, don alkali ya tabbatar masu da takarar su.
Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya idan Bashir Machina ya garzaya Kotu da sakamakon zaben fidda gwani na Yobe ta Arewa inda ya samu kuri'u 289.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: