Washington, DC - A wata hira da Muryar Amurka, Dr. Christopher Piwuna mataimakin shugaban kungiyar ASUU ta kasa, ya bayyana cewa bayan wani zama na kwamitin shugabannin kungiyar ne suka yanke shawarar tsawaita yajin aikin. Ya kuma ce babban Ministan Ilimin Najeriya, Chris Ngige da karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba sun nuna wa ‘yan Najeriya cewa batun ilimi ba shi suka sa a gaba ba, hakazalika ita ma Gwamnatin Tarayya ta nuna cewa batun zaben 2023 ne a gabanta.
Kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ta dauki alkawarin shiga tsakani, a cewar Dr. Piwuna, ya kara da cewa suna fata nan da sati daya ko biyu zasu janye yajin aikin idan suka cimma matsaya.
Malaman sun shiga yajin aikin ne saboda gwamnati ta gaza wajen aiwatar da wata yarjejeniya da ta sanya wa hannu a shekarar 2020, ta neman sabunta wata yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar ASUU a shekarar 2009.
A watan Fabarairu ne dai aka fara yajin aikin na gargadi yanzu kuma an tsawaita shi zuwa watan Agustan wannan shekarar ta 2022 muddin gwamnati ba ta biya wa kungiyar bukatunta ba.
Daliban jami’a a Najeriya sun yi Allah wadai da wannan mataki da suka ce zasu yi zanga zangar nuna rashin amincewa da shi.
Dr. Piwuna ya ce sun damu da halin da daliban ke ciki, amma suna yajin aikin ne don ganin gwamnati ta inganta ilimi a matakin jami’a. Ya kara da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki batun ilimi da muhimmanci a Najeriya.
Saurari cikakkiyar hirar Halima AbdurRa’uf da Dr. Piwuna.