Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Kanshin Gaskiya A Zargin Da El-Rufa'i Ya Yi Na Neman Kada Jam'iyyar APC-Lai Mohammed


Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta maida martani kan zargin da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-rufa'i ya yi na cewa wadansu hadiman gwamnati a fadar shugaban kasa suna yi wa jam'iyyar zagon kasa don hana ta samun nasara a zaben da ke tafe.

A wata hira da manema labarai a Fadar Shugaban kasa, Ministan yada labarai Lai Mohammed, ya nanata matsayin shugaban kasa na cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali ne kawai wajen tabbatar da an yi sahihin zabe ba tare da nuna goyon baya ko tauye wani ba.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa wasu a fadar shugaban Najeriya na kokarin hana jam’iyyar APC da dan takararta na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, samun nasara a zaben shugaban kasa da za a yi a wannan watan.

Zaben Najeriya/ Bola Tinubu
Zaben Najeriya/ Bola Tinubu

El-Rufai ya bayyana hakan ne ranar Laraba a lokacin wata hira da gidan Talabijin na Channels.

Gwamnan ya jaddada cewa, wadannan mutanen suna so dan takararsu ya yi nasara a zaben fidda gwani na shugaban kasa, amma bai ci zaben ba.

Ya kara da cewa mutanen na kokarin ganin jam’iyya mai mulki da Tinubu sun fadi zabe.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, wasu a fadar shugaban na kokarin fakewa da burin shugaba Buhari na yin abin da ya ke ganin ya dace don su dakile damar jam’iyyar.

Game da batun canza fasalin kudin Najeriya, El-Rufai ya fadi cewa bai kamata sauran jama’a su wahala ba saboda matakin, ko tsarin ya sa jama’a su ji haushin jam’iyyar APC tunda ba ra’ayin jam’iyyar ko na dan takararta ba ne, ra’ayi ne na wasu a fadar shugaban kasa, a cewarsa.

Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

Ya kuma ce ya kamata jama’a su sani tsarin sauya fasalin kudi ba na gwamnan babban bankin Najeriya ba ne, don ko a lokacin mulkin soja shugaba Buhari ya dauki matakin a asirce da nufin kama masu sama da fadi da dukiyar al’uma.

Gwamnan ya ce ko da yake shugaban na da ikon sake fasalin kudi, yin hakan a daidai wannan lokaci ba shi da fa’ida ta bangaren siyasa ko tattalin arziki.

Kalaman na El-Rufai dai na zuwa ne mako guda bayan da dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ya ce akwai wani shiryayyen kulli na hana shi cin zabe.

Sai dai gwamnatin tarayya ta maida martani ne kan zargin da gwamna Nasir El-Rufai ya yi, ba abin da dan takarar jam'iyyar ya fada a wajen yakin neman zabe ba.

Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed (Twitter/@FMIC)
Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed (Twitter/@FMIC)

A lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar gwamnati a yayin wani taron majalisar zartarwa ta tarayya da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba, Ministan yada labarai Lai Mohammed ya kuma ce idan har akwai wanda ke neman dakile wani dan takara, to a hukumance gwamnati bata san da shi ba.

Saurari Rahoton Babangida Jibrin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG