WASHINGTON, DC - Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan wasu masu ibada a coci sannan suka tada bam a cocin ta katolika da ke kudu maso yammacin Najeriya ranar Lahadi 5 ga watan Yuni, ana kyautata zato mutane da yawa sun mutu, kamar yadda ‘yan majalisar dokokin jihar suka bayyana a cewar kamfanin dillancin labaran AP.
Maharan sun kai harin ne a majami'ar St. Francis Catholic Church da ke jihar Ondo a lokacin da jama’a suke ibada, a cewar dan majalisa Ogunmolasuyi Oluwole. Cikin wadanda suka mutu har da yara da yawa, a cewar shi.
An kuma sace limamin cocin, a cewar Adelegbe Timileyin, wanda ke wakiltar yankin Owo na jihar.
A ranar Lahadin, gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya rubuta a shafinsa na twitter cewa "zukatan mu na cike da juyayi.” Ya kara da cewa "makiyan jama'a sun kai hari kan zaman lafiya da kwanciyar hankalin mu."
Nan take dai hukumomin yankin ba su fadi adadin wadanda suka mutu ba a hukumance. Amma Timileyin ya ce an kashe akalla mutane 50, ko da yake wasu sun ce adadin ya zarta haka, a cewar AP.