WASHINGTON, DC - Sanata Datti Baba Ahmed mataimakin dan takarar shugaban kasa Peter Obi a karkashin jam’iyyar Labor, wanda kuma ya kafa jami’ar Base da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce in Allah ya yarda ba za a ji batun yajin aiki ba idan jam’iyyarsu ta lashe zabe a shekarar 2023.
A wata hira ta musamman da shugaban sashen Hausa na muryar Amurka Aliyu Mustapha, Datti ya ce ko kadan bai ga inda malaman suka yi zari ba. Ya kara da cewa in dai akan malaman makaranta ne da jami’an tsaro, yana goyon bayan a biya musu bukatunsu ko ma a linka sosai.
Sama da wata shida kenan daliban jami’a a Najeriya ke gida sakamakon yajin aikin da malamansu ke yi, abinda Datti ke gani taurin kan gwamnati da rashin maida hankali ne ya sa har yanzu aka yi kiki-kaka wajen samun daidaito. Ya kamata shugaban kasa ya tabbatar an kawo karshen yajin aikin a kuma dauki matakin ganin hakan bai zai sake faruwa ba, a cewarsa.
“In Allah ya yarda muka kafa gwamnati, zan roki shugaba Obi ya jagoranci kokarin warware matsalar. Bayan an biya bukatun malaman madaidaita, za a cimma yarjejeniya da su kan cewa ba zasu yi yajin aiki ba cikin shekaru akalla hudu, saboda ba karamar illa yajin aikin malamai ke janyowa ba ga dalibai " a cewar Datti.
Batun sa-in-sa tsakanin kungiyar malaman jami’a ta ASUU da gwamnatin tarayyar Najeriya wani abu ne da aka kwashe shekaru ana fama da shi a kasar wanda lokuta da yawa yake kai ga yajin aikin malamai na lokaci mai tsawo, saboda har yanzu shugabannin sun kasa biya wa malaman tarin bukatunsu, ko da yake wasu na gani kungiyar malaman na yin zari.
Saurari cikakkiyar hirar Aliyu Mustapha.