Konturolan ya ce sun kuma cafke wasu maharan suna kuma ci gaba da gudanar da bincike.
Ita ma rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ce ta yi nasarar cafke fursunoni guda tara da suka yi yunkurin tserewa bayan da ‘yan bindigar suka fasa gidan yarin.
Wani mazaunin Jos, Tanko Yusuf ya ce tun da farko ya kamata jami’an tsaro su sa matakan dakile harin saboda sakonnin da suka yi ta yawo na cewar Boko Haram za su kawo hari a jihar Filato.
Mai fashin baki kan lamuran yau da kulum, Hamisu Doguwa, ya ce yadda ake barin fursunoni suna rike wayar salula a cikin gidan yari, shi ke zama matsala.
Gwamnatin jihar Filato, wacce ta yi tir da harin, ta kuma ce dole sai an dauki kwararan matakan kawo karshen yawan hare-hare da ake kai wa a gidajen yarin Najeriya.
Saurari rahoton Zainab Babaji.