A zagayen da ya yi a karshen makon da ya gabata a manyan asibitocin birnnni Yamai da cibiyoyin kwantar da masu fama da cutar corona, Ministan kiwon lafiyar al’umma, Iliassou Idi Mainassara ya bayyana cewa daga wannan mako za a soma tambayar likitoci takardar shaidar allurar rigakafin corona a mashigar asibitoci da nufin ba su kariya daga wannan cuta.
A jajibirin shudewar wannan wa’adi, kungiyar kananan likitoci wato SUSAS ta fitar da sanarwar watsi da matakin. kamar yadda sakataren tsare tsaren wannan kungiya, Muddaha Awache ya bayyana.
Su ma daliban dake karatu a fannin likitanci a Jami’ar AbdoulMoumouni ta Yamai sun bijire wa umurnin na hukumomin kiwon lafiya saboda a cewarsu matakin ya saba wa ka’idodin aiki kamar yadda suka bayyana a wata sanarwa. Zakari Mai Kassoum shi ne shugaban kungiyar wadannan dalibai.
Mutane 6,974 ne suka kamu da cutar covid 19 tun daga farkon bullar wannan cuta a Nijer a watan Maris na 2020 kawo jiya Lahadi 28 ga watannan na Nuwamban 2021, yayin da 254 daga cikinsu suka rasu sai wasu 154 dake shan magani a halin yanzu, wadanda 32 daga cikinsu ke kwance a asibiti, inji rahoton sakatariyar ma’aikatar lafiya ta kasa wace tace ko a jiya Lahadi an gano mutane 16 da suka harbu da kwayar cutar.