Hukuncin na nufin yanzu jihohi ne ke da hurumin su yi gaban kansu kan wannan batu, imma su haramta ko su halalta.
Ita dai hukumar ta EFCC ta shigar da kara akan wani gida da aka saya mai suna Guinea House da ke layin Marine Road a Apapa a jihar ta Legas akan kudi naira miliyan 805.
A ranar 13 ga watan Yuli shirin karin kudin tikitin da aka yi zai fara aiki a daukacin jihar.
“Muna daukan matakan magance korafe-korafe dukkan mambobin jam’iyya. Hadin kanmu shi ne muhimmin abu a gare ni.
“Na san cewa, na yi iya bakin kokarina wajen ganin abubuwa sun daidaita, amma daga karshe na gane cewa, al'amura sun riga sun rincabe.” In ji Bello.
“Zan tuntubi kakakin majalisar wakilan Birtaniya, domin mu tabbatar an yi wa Ekweremadu adalci." In ji Gbajabiamila.
Shugaban na Najeriya dai bai ambaci ma'aikatun da zai tura ministocin ba a cikin wasikar da ya aikewa majalisar dattawan a ranar Talatar makon jiya.
A karshen makon da ya gabata Gwamna Bello Matawalle ya bayyana shirinsa na fara ba da lasisin mallakar bindiga, a wani mataki na ba al’umar jihar damar kare kansu.
“Mun yi nasara a tattaunawar da muka yi da shugaban kasa, saboda haka, yanzu batun ficewa daga jam’iyyar ya wuce.” In ji Kalu.
Buhari ya kai ziyarar ce bisa gayyatar Shugaban kasar Portugal, Marcelo Rebelo de Sousa.
“Shawarar da mai shari’a Tanko Muhammad ya yanke ta yin murabus daga mukaminsa na Alkalin alkalan Najeriya, abin a yaba ne.” In ji Atiku.
Sai dai ‘yan jam’iyyar adawa ta Republican a majalisar dokokin kasar, sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan bukata da Biden ya gabatar, suna masu cewa, ba za ta yi wani tasiri ba.
A ranar Juma'a a 24 ga watan Yuni za a bude taron a hukumance, a kuma ranar Lahadi ake sa ran Shugaba Buhari zai koma Najeriya.
Wannan shi ne zaman jin bahasi na bakwai da majalisar ke gudanarwa a binciken ke zargin Trump da yunkurin ganin an sauya sakamakon zaben na 2020.
Sai dai akwai yiwuwar wannan kuduri ya samu cikas daga bangaren 'yan majalisar dattawa a na 'yan Democrat da Republican wadanda suka fi mayar da hankulansu kan tsaurara matakan tsaro da kula da lafiyar kwakwalwa.
‘Yan sanda sun ce dan bindigar ya bude wuta a asibitin ne, bayan da ya dora laifin wani matsanancin ciwo baya da ya yake fama da shi tun bayan wata tiyata da aka masa a asibitin.
Harin wanda aka kai a garin Uvalde a jihar ta Texas, na zuwa ne kasa da makonni biyu da harin da wani dan bindiga ya kai a wani kanti a garin Buffalo da ke New York, wanda ya halaka mutum 10.
Wannan hari, ya sake ta da muhawara kan kiraye-kirayen samar da dokokin da za su takaita mallakar makamai cikin sauki a Amurka.
A ranar Lahadi, Man City za ta kara da Aston Villa yayin da Liverpool za ta fafata da Wolves.
“An gama wasan! Maraba da zuwa jam’iyyar NNPP Sanata Ibrahim Shekarau.” Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar ta NNPP Abdulmumin Jibrin ya rubuta a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Domin Kari