Kungiyoyin Manchester City da Liverpool na haroro kofin gasar Premier League yayin da suke saman teburin gasar da tazarar maki daya tal.
City na saman teburin da maki 90 yayin da The Reds take da maki 89.
Liverpool ta farfado da burinta na lashe kofin gasar bayan da ta lallasa Southampton da ci 2-1 a wasan da suka buga a ranar Talata.
Yanzu wasanni biyu ne za su fayyace kungiyar da za ta lashe wannan Kofi.
A ranar Lahadi, Man City za ta kara da Aston Villa yayin da Liverpool za ta fafata da Wolves.
Wadannan wasannin da za a buga a ranar Lahadi 22 ga watan Mayu, musamman tsakanin Man City da Aston Villa su ne za su nuna wanda zai daga kofin.
Ga Yadda Lissafin Yake:
- Idan Man City ta lashe wasanta da Aston Villa, ya zama ta lashe kofin Premier.
- Idan Man City ta tashi da kunnen doki ko ta sha kaye a hannun Aston Villa, Liverpool kuma ta ci wasanta da Wolves, ya zama Liverpool ce za ta lashe kofin
- Idan City ta yi kunnen doki da Aston Villa, Ita ma Liverpool ta yi kunnen doki da Wolves, ya zama City ce ta lashe kofin
Duk da wannan lissafi, masu sharhi dai a fagen kwallon kafa na ganin, komai yana hannun Man City a wannan lalen.
Idan kuma ta lashe wasanta da Villa, ya zama ta lashe kofin na Premier sau hudu cikin shekara biyar.