Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya jaddada matsayarsa ta cewa ba zai nemi yin tazarce ba, yana mai cewa zai bi tsarin da kundin mulkin Najeriya ya zayyana.
Buhari ya bayyana hakan ne a gefen taron koli na kasashen da Ingila ta rena wanda ke gudana a Kigali, babban birnin Rwanda yayin da suke ganawa da Firaministan Birtaniya Boris Johnson, kamar yadda wata sanarwa da kakakin Buhari Femi Adesina ya fitar da yammacin ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce, Johnson ya tambayi Buhari ko zai sake tsayawa takara, sai shugaban na Najeriya ya kada baki ya ce, “ni na yi wani wa’adi? A’a! Mutum na farko da ya gwada yin hakan bai wanye lafiya ba.”
Wannan amsa da Buhari ya ba Johnson, kamar yadda sanarwar ta fada, ya sa dukkansu suka bushe da dariya.
A cewar sanarwar, “ga dukkan alamu, Firai ministan bai da cikakkiyar masaniya kan iya adadin wa’adin mulkin da mutum ya kamata ya yi,” a shugabancin Najeriya.
A ranar 29 ga watan Mayu, wa'adin mulkin shugaba Buhari na biyu zai kare.
Wa'adin mulki biyu na tsawon shekaru hudu-hudu kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba dama a kowa ya yi na shugabancin kasar.
Taron Kasashen renon Ingila wanda ake wa lakabi da CHOGM a takaice ya mayar da hankali ne wajen duba fannonin da za a bunkasa kasashe 54 da suka kasance mambobi a kungiyar kasashen da Ingila ta rena.
Shugaban na Najeriya zai hadu da sauran takwarorinsa da suka fito daga nahiyar Afirka, Asiya, Turai da kuma yankin Amurka don tattauna batutuwan da za su shafi rayuwar sama da mutum biliyan biyu da ke kasashe 54.
A ranar Juma'a a 24 ga watan Yuni za a bude taron a hukumance, a kuma ranar Lahadi ake sa ran Shugaba Buhari zai koma Najeriya.