Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Legas Ta Kara Naira 100 Akan Kudin Tikitin Motocin Safa Na BRT


Tashar motocin BRT a Legas (Hoto: Facebook/Babajide Sanwo-Olu)
Tashar motocin BRT a Legas (Hoto: Facebook/Babajide Sanwo-Olu)

A ranar 13 ga watan Yuli shirin karin kudin tikitin da aka yi zai fara aiki a daukacin jihar.

Gwamnatin Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta kara naira 100 akan kudin tikitin motocin bas na safa da ake kira BRT, wadanda ke zirga-zirga a sassan jihar.

Karin zai shafi dukkanin hanyoyin da motocin ke bi kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Hukumar kula da sufurin motocin bas na LAMATA ne suka sanar da wannan kari a wata sanarwa da suka fitar a ranar Alhamis.

A ranar 13 ga watan Yuli karin zai fara aiki a cewar sanarwar.

Hukumar ta LAMATA ta ce gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya amince da wannan kari wanda zai shafi dukkan hanyoyin da motocin ke bi.

A cewar sanarwar, an yi karin ne saboda tsadar man dizel da kuma karancin sassan da ake gyaran motocin.

Yanzu tafiya daga Ikorodu zuwa TBS ya koma naira 600 a maimakon 500, Berger zuwa Ajah ya koma 700 maimakon 600.

Kazalika tafiyar daga Oshodi zuwa Abule Egba za a biya naira 450 maimakon 350 sannan za a biya naira 600 daga Abule-Egba-CMS-Obalande maimakon naira 500.

XS
SM
MD
LG