Majalisar Wakilan Najeriya na tantance sabbin ministoci bakwai da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zaba.
A makon da ya gabata, Buhari ya mika sunayen ministocin wadanda za su maye gurbin ministocin da suka ajiye aikinsu saboda yin takara a zaben 2023.
Dokar zaben Najeriya ta 84 (12) ta harmata wani mai rike da mukamin nadi ya tsaya takara ba tare da ya sauka a kujerarsa ba.
Ministocin da aka zaba, sun hada da, Henry Ikechukwu Ikoh daga jihar Abia, Umana Okon Umana daga Akwa Ibom, Ekumankama Joseph Nkama daga Ebonyi, sai Goodluck Nanah Opiah daga jihar Imo.
Sauran sun hada da Umar Ibrahim El-Yakub daga Kano, Ademola Adewole Adegoroye daga Ondo State da Odum Udi daga jihar Rivers State.
Shugaban na Najeriya dai bai ambaci ma'aikatun da zai tura ministocin ba a cikin wasikar da ya aikewa majalisar dattawan a ranar Talatar makon jiya.
Ministan sufuri Rotimi Amaechi da minsitan Niger Delta Godswill Akpabio, na daga cikin ministocin da suka yi murabus don yin takarar shugaban kasa a zaben 2023.