Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Tuntubi Birtaniya Kan Ekweremadu


Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Hoto: Facebook/Majalisar Wakilai)
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila (Hoto: Facebook/Majalisar Wakilai)

“Zan tuntubi kakakin majalisar wakilan Birtaniya, domin mu tabbatar an yi wa Ekweremadu adalci." In ji Gbajabiamila.

Majalisar Wakilan Najeriya, za ta tuntubi takwarar aikinta ta Birtaniya dangane da tuhumar da hukumomin Birtaniya suke yi wa Sanata Ike Ekweremadu da mai dakinsa Beatrice kan yunkurin sayen wani sashin jikin dan adam.

A makon da ya gabata, ‘yan sanda London suka tsare Ekweremadu tare da matarsa bayan da suka ce sun gano sanatan yana yunkurin a yi wa wani matashi dan Najeriya aiki don a cire wani sashen jikinsa, lamarin da suka ce ya sabawa dokar kasar.

Rahotanni sun nuna cewa Ekweremadu na da diya mai fama da cutar koda, kuma ciwon ya yi tsananin da sai an yi mata dashe.

A zaman da majalisar ta wakilan ta Najeriya ta yi a ranar Talata, Abdullahi Sa’ad Abdulakadir mai wakiltar mazabar Ningi/Warji a jihar Bauchi, ya gabatar da wannan kuduri kan majalisar ta dauki mataki, kudurin da ya samu karbuwa a wajen sauran mambobin majalisar.

An dai yi mahawara kan batun inda mambobi suka yi ta nuna goyon bayansu kan lamarin, daga karshe kuma Kakakin majalisar Femi Gbajabiamila, ya ce za su dauki mataki akai domin ganin an yi wa Ekweremadu adalci.

“Zan tuntubi kakakin majalisar wakilan Birtaniya, wanda a ‘yan watanni baya na gana da shi, domin mu tabbatar an yi wa Ekweremadu adalci.

“Akwai bukatar mu nuna damuwarmu kan wannan batu ta hanyar diflomasiyya.” In ji Gbajabiamila.

Gbajabiamila ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji saurin yanke hukunci kan lamarin yana mai cewa, mutum ba ya zama mai laifi har sai hukuma ta shi da laifin.

Bayanai da suka yi ta bayyana bayan tsare Ekweremadu, sun nuna cewa Sanatan ya nemi iznin ofishin jakadancin Birtaniya, ya kuma bi ka’idojin da aka gindaya don zuwa da matashin mai suna David Birtaniya don ya ba da gudunmowar kodarsa ga ‘yar Ekweremadu.

A ranar 7 ga watan Yuli kotun Majistiret da ke sauraren karar a West London, za ta ci gaba da shari’ar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG