Lamarin dai ya faru ne a lokacin da Chris Rock cikin barkwanci ya yi ba’a akan yanayin gashin kan matar Will Smith, Jada, wacce a baya-bayan nan ta aske kanta kusan tal kwabo, saboda wata larura da take damunta da ake kira Alopecia wacce ke haifar da zubewar gashi.