Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yi Hattara Kan Batun Ba Mutane Dama Su Mallaki Bindiga - Janar Danbazau 

Tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Janar Abdulrahman Danbazau mai ritaya (Hoto: Facebook/Ma'aikatar Cikin gida ta Najeriya)
Tsohon babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Janar Abdulrahman Danbazau mai ritaya (Hoto: Facebook/Ma'aikatar Cikin gida ta Najeriya)

A karshen makon da ya gabata Gwamna Bello Matawalle ya bayyana shirinsa na fara ba da lasisin mallakar bindiga, a wani mataki na ba al’umar jihar damar kare kansu.

Tsohon shugaban sojin kasa na Najeriya, Janar Abdulrahman Danbazau mai ritaya, ya ce akwai bukatar a yi takatsantsan kan yunkurin da ake yi na barin mutane su mallaki bindiga.

Danbazau na magana ne kan matsayar da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka na shirin ba al’umar jihar damar su mallaki bindiga don kare kansu.

Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta zama tungar ‘yan ta’adda, wadanda ke kai hare-hare akan kauyuka a duk lokacin da suka bushi iska, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

A karshen makon da ya gabata Gwamna Bello Matawalle ya bayyana shirinsa na fara ba da lasisin mallakar bindiga, a wani mataki na ba al’umar jihar damar kare kansu.

“Yanzu misali, za ki ga dan ta’adda ya shigo gari da ke mutum dubu 20 ko 30, akwai matasa majiya karfi a garin nan, sun kai kila dubu goma, amma sai ki ga yaro biyar sun zo da bindigogi, sun zo sun tarwatsa garin, saboda mutane ba su da umarnin da za su rike makami.”

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle (Facebook/Zamfara Dep Governor)

Sai dai lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya inda jami’an gwamnati da masana tsaro ke ta sharhi kan lamarin.

A cewar Danbazau, idan aka yi haka, za a karawa masu miyagun ayyuka karfi, inda masu kananan sace-sace da ke amfani da wukake, za su iya yada wukaken su koma mallakar bindigar.

“Amma na yarda hakkin ne a wuyan gwamnati ta zauna ta kare lafiyar mutane da dukiyarsu.” In ji Danbazau.

Sai dai tsohon babban hafsan sojin kasar ya ce akwai bukatar a hattara wajen daukar wannan mataki.

“Duk abin da za ka zauna ka yi shi cikin fushi sai ka yi da na sani. Ba shakka mutane suna cikin fargaba, mutane suna so su ga karshen wannan abu, amma a san irin matakin da za a dauka.” Danbazau ya kara da cewa.

XS
SM
MD
LG