Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gana da sanatocin jam’iyyar APC 22 da ke barazanar ficewa daga jam’iyyar.
Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawan kasar, Sanata Orji Uzor Kalu ne ya jagoranci sanatocin zuwa fadar shugaban kasar a ranar Talata.
A cewar Kalu, jam’yyar mai mulki ta kamo bakin zaren barakar da ke sa sanatocin suke yunkurin ficewa daga APC.
Rahotanni sun ce jam’iyyar adawa ta PDP suke shirin komawa.
“Na jagoranci sanatoci 22 da ke korafi da sauran mambobin jam’iyyar APC zuwa gaban Shugaba Muhammadu Buhari.
“Mun yi nasara a tattaunawar da muka yi da shugaban kasa, saboda haka, yanzu batun ficewa daga jam’iyyar ya wuce.” In ji Kalu, wanda ya wallafa wannan sanarwa hade da hotunan sanatocin tare da Shugaba Buhari a fadarsa.
Tun bayan da aka kammala zabukan fitar da gwani a jam’iyyun siyasar Najeriya, masu takara da dama da ba su yi nasaraba, sun yi ta nuna korafi musamman a jam’iyyar APC, kan yadda aka gudanar da zabukan.
A makon da ya gabata, rahotannin sun yi nuni da cewa tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya Fani Kayode, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar ta APC da su tashi tsaye, domin wasu sanatoci 22 na shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa PDP.
Akalla sanatoci bakwai ne suka ficewa daga jam’iyyar ta APC ya zuwa yanzu.
Majalisar Dattawan Najeriya na da sanatoci 109, 65 daga cikinsu ‘yan jam’iyyar APC ne kafin tasowar wannan guguwar sauya sheka da ta biyo bayan zabukan fitar da gwani.