Wannan adadi ya kai jimullar sunayen da Tinubu ya aikawa majalisar zuwa 47 yayin da sabuwar gwamnatin ta doshi wata uku da karbar mulki.
“Tun jiya (Talata) Najeriya ta katse babbar hanyar layin da take samar wa Nijar wuta.” Wata majiya a kamfanin wutar lantarki na Nigelec ta fadawa AFP.
Ganawar ta Blinken da Bazoum na zuwa ne yayin da sojojin da suka yi juyin mulki suka nada gwamnoni a jihohi takwas da ke kasar.
Zanga-zangar ta adawa ce da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wadanda kungiyoyin suka ce sun jefa al'umar kasar cikin kangin rayuwa.
Ita dai Ingila ta lashe wasannin uku a jere ba tare da ta shan kaye ba, yayin da ita kuma Najeriya ta yi canjaras sau biyu ta kuma shammaci Australia da ci 3-2.
Tinubu ya kuma jinjinawa kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu da suka riga suka yi karin albashi.
Sai dai sanarwar ba ta ambaci takamaiman dalilin da ya sa shugaban wanda ya karbi mulki a watan Mayu zai yi jawabin ba.
A ranar Laraba 26 ga watan Yuli, sojojin da ke tsaron lafiyar shugaban Nijar Mohamed Bazoum suka kaddamar da shirin karbe ragamar mulkin kasar.
Shi dai Obi a birnin Jos ya girma, kuma ya fara wasan kwallonsa ne a garin inda daga baya ya shahara.
Blinken ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Bazoum ta wayar tarho a ranar Laraba.
Kungiyar ECOWAS da AU da Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira da a saki Bazoum cikin gaggawa ba tare da gindaya wasu sharudda ba.
Yan Najeriya sun jima suna dakon fitar da jerin sunayen ministocin yayin da wa’adin da doka ta tanada na mika sunayen ya zo karshe.
Wannan mataki ya biyo bayan ziyarar da Shugaba Talon ya kai wa Tinubu a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba.
Cikin wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta yi kira ga dakarun da ke da hannu a yunkurin juyin mulki da su hanzarta sakin shugaban kasar saboda an zabe shi ne bisa tsarin mulkin dimokradiyya.
“Bayanai na nuni da cewa Shugaba Mohamed Bazoum na hannun dogarawan fadarsa." In ji wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.
Hatsaniyar ta kaure ne a lokacin da jami’an gidan yari da na hukumar farin kaya ta DSS suka fara kai ruwa rana kan wanda zai tafi da Emefiele bayan da aka kammala zaman kotun.
“Ina mai matukar farin cikin fara wannan tafiya da abin kaunata …. Mata da miji na nan tafe.” In ji Bishara.
Tuni dai Davido ya cire bidiyon a shafukansa na sada zumunta bayan da aka yi ta sukar shi a dandalin yanar gizo.
Domin Kari