Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Tura Karin Sunayen Ministoci 13 – Gbajabiamila


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu lokacin bude taron kaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu lokacin bude taron kaddamar da majalisar tattalin arzikin kasa

Yan Najeriya sun jima suna dakon fitar da jerin sunayen ministocin yayin da wa’adin da doka ta tanada na mika sunayen ya zo karshe.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayyar Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce nan ba da jimawa ba, za su sake tura karin sunayen minisoti 13 ga Majalisar Dattawan kasar.

A ranar Alhamis Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen mutum 28 da zai nada a matsayin ministoci.

‘Yan Najeriya sun jima suna dakon fitar da jerin sunayen ministocin yayin da wa’adin da doka ta tanada na mika sunayen ya zo karshe.

A cewar Gbajabiamila, akwai yiwuwar shugba Tinubu ya kirkiri wasu sabbin ma’aikatu kamar ydda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.

Hakan a cewar Gbajabiamila kokari ne na sa kowace ma’aikata ta ci gashin kanta ba tare da an cakuda su ba.

Ga jerin sunayen mutum 28 da fadar shugaban Najeriyar ta fara mikawa Majalisar Dattawa kamar yadda Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya karanto su:

Abubakar Momoh, Yusuf Maitama Tuggar, Ahmed Dangiwa, Hannatu Musawa, Uche Nnaji, Betta Edu, Doris Uzoka, David Umahi, Ezenwo Nyesom Wike, Muhammed Badaru Abubakar da Nasir El-Rufai.

Sauran sun hada da Ekperipe Ekpo, Nkeiruka Onyejocha, Olubunmi Tunji Ojo, Stella Okotette, Uju Kennedy-Ohanenye, Bello Muhammad Goronyo, Dele Alake, Lateef Fagbemi da Mohammad Idris,

Har ila yau an mika sunayen Olawale Edun, Waheed Adebayo Adelabu, Imman Suleiman Ibrahim, Ali Pate, Joseph Utsev, Abubakar Kyari, John Enoh da Sani Abubakar Danladi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG