Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Da Suka Yi Juyin Mulki Sun Bayyana Sabon Shugaban Nijar


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Rundunar sojin da suka jagoranci juyin mulki a Jamhuriyar Nijar ta bayyana Janar Abdouramane Tchiani a matsayin sabon shugaban kasar.

A ranar Laraba 26 ga watan Yuli sojoji suka ayyana kifar da gwamnatyin Shugaba Mohamed Bazoum.

Har yanzu Bazoum na hannun sojojin da suka yi juyin mulki.

Kungiyar ECOWAS da AU da Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira da a saki Bazoum cikin gaggawa ba tare da gindaya wasu sharudda ba.

A ranar Juma’a Tchiani ya yi jawabi da al’umar Nijar inda ya zayyana dalilan da suka sa suka karbe mulki a hannun Bazoum.

Matsalar tabarbarewar tsaro, rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasa, na daga cikin dalilan da Tchiani ya lissafo a jawabinsa.

“Ba zai yi wu mu ci gaba da tafiya a haka ba.” Janar Tchiani ya ce.

A shekarar 2021 aka zabi Bazoum bayan da ya lashe zaben a zagaye na biyu karkashin jam’iyyar PNDS mai mulki, inda ya gaji tsohon Shugaba Issouhou Muhamadou.

A watan Maris din 2021 – kwana biyu kafin a rantsar da Bazoum, wasu sojoji suka yi yunkurin yin juyin mulki – amma ba su yi nasara ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG